• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu na so jama’a su ƙara haɗa kai yayin da Nijeriya ke cika shekara 65 da zama ’yantacciya

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
September 26, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu na so jama’a su ƙara haɗa kai yayin da Nijeriya ke cika shekara 65 da zama ’yantacciya
Ministoci, Etsu Nupe da sauran jama'a a lokacin sallar Juma'ar a Babban Masallacin Ƙasa a Abuja a yau

Ministoci, Etsu Nupe da sauran jama'a a lokacin sallar Juma'ar a Babban Masallacin Ƙasa a Abuja a yau

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da zaman lafiya domin cigaban ƙasa baki ɗaya.

Wata sanarwa da Dakta Suleiman Haruna, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ya sanya wa hannu, ta ce Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, a lokacin sallar Juma’a ta musamman da aka shirya a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai.

Shugaban Ƙasa, wanda Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya wakilta, ya bayyana cewa Nijeriya za ta iya cika mafarkin ubannin ƙasa ne kawai idan ’yan ƙasa sun zauna cikin zaman lafiya, sun jure bambance-bambancen su, kuma sun dage wajen aiki tuƙuru.

Jama’a suna sauraren huɗubar liman

Ya ce: “A ko yaushe akwai bambance-bambance, amma saƙon Shugaban Ƙasa na fata, haɗin kai da zaman tare ne. Dole ne dukkan ’yan Nijeriya su rungumi waɗannan ɗabi’u yadda tare za mu samu cigaba da wadata da Shugaban Ƙasa ya yi alƙawari tun bayan hawan sa mulki.”

Ya ƙara da cewa ko da yake ƙasar nan tana cikin wani yanayi na sauyi, gwamnatin Tinubu tana samun cigaba a hankali wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta.

Ya yi kira ga ’yan ƙasa da su yi haƙuri yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin juya halin da tattalin arzikin ƙasa yake ciki.

Alhaji Mohammed Idris, wanda shi ne Kaakaki Nupe, yana gaisawa ga Mai Martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, a Babban Masallacin Ƙasa a Abuja

Yayin da yake taya ’yan Nijeriya murnar cikar ƙasar nan shekara 65 da samun ’yancin kai, Shugaban ya roƙe su da su ci gaba da yin addu’a ga shugabanni da ƙasa domin samun makoma mai haske.

Dangane da taken bikin na bana, wato “Nijeriya a 65: A Haɗa Kai Don Gina Ƙasa Mafi Girma,” ministan ya ce Shugaban Ƙasa na kira ga ’yan Nijeriya gaba ɗaya, ba tare da la’akari da ƙabila, addini, bambancin siyasa ko matsayi ba, da su haɗa kai domin gina Nijeriya wadda muke mafarki da ita.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a masallacin

Ya kuma lissafa wasu nasarori da gwamnatin Tinubun ta samu, inda ya ce Nijeriya ta samu gagarumin cigaba a ɓangarorin tattalin arziki, tsaro, noma, da kuma wasu muhimman sassa.

Ya ce: “Abin da ake buƙata yanzu shi ne ’yan Nijeriya su yi aiki tare.”

Ya kuma yi wa al’ummar ƙasa fatan a yi bukin cikin zaman lafiya da murna.

Ministan Noma da Bunƙasa Karkara, Alhaji Mohammed Abubakar Kyari, wanda ya halarci sallar Juma’ar, ya ce Nijeriya tana kan hanyar dawo da martabar da ta rasa a idon ƙasashen duniya.

Shi kuma Etsu Nupe wanda shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, wanda tare da shi aka yi sallar, ya yi kira ne da a zauna lafiya, kuma ya yi addu’ar samun wadata da cigaban ƙasa a wannan cikar Nijeriya shekara 65 da zama ‘yantacciya.

Tags: 'yan Nijeriya'yancin kan ƙasaBabban Masallacin ƘasaEtsu Nupehaɗin kaiMohammed Abubakar KyariMohammed Idrissallar Juma'aShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Ganawa da Guterres: Nijeriya ta jaddada neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Next Post

Nijeriya tana kan hanyar kaiwa ga ƙarfin arziki mai ɗorewa, inji Tinubu

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post

Nijeriya tana kan hanyar kaiwa ga ƙarfin arziki mai ɗorewa, inji Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!