An kama mutum goma sha biyu, ciki har da ‘yan Nijeriya takwas, a ƙasar Kanada bisa tuhumar gudanar da wata ƙungiyar satar motoci da ‘yan sanda suka ce sun ƙwato motoci 96 da aka sace a hannun su, waɗanda darajar su ta kai dala miliyan 4.5, waɗanda kuma ake shirin tura su Afirka ta Yamma.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan yankin Peel da ke Ontario ce ta sanar da kamen a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na intanet a ranar Litinin.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin suna fuskantar tuhume-tuhume 231 bayan wani bincike kan sata da fitar da manyan motoci ƙirar SUV masu tsada, da motocin ɗaukar kaya, da sauran motoci masu daraja da aka ɓoye a cikin kwantenonin jigilar kaya.
An fara binciken, wanda aka yi wa laƙabi da Project Cadetta, a watan Maris na 2026 tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Iyakokin Kanada (CBSA).
Da farko binciken ya mayar da hankali ne kan wata ma’ajiyar kaya da ke Brampton, Ontario, wadda ake zargin ana amfani da ita wajen tara motocin da aka sace kafin a shirya jigilar su zuwa Afirka ta Yamma ta tashoshin jiragen ruwa na Kanada.
‘Yan sandan sun ce binciken ya kuma gano wata babbar ƙungiyar masu laifi da ke aiki a faɗin Babban Yankin Toronto da yankunan maƙwabta.
A cewar ‘yan sandan, mutum biyar manyan waɗanda ake zargi ne suka jagoranci satar motocin, da tuƙa su, da fitar da su, yayin da sauran waɗanda ake tuhuma suka taimaka wajen samar da wuraren dakon kaya, da ɗaukar kwantena, da safarar motocin da aka canza lambobin tantance su.
‘Yan sandan sun ce an samo motoci 96 da aka ƙwato a ɓoye cikin kwantenonin jigilar kaya.

Takardar tuhumar da ‘yan sandan suka fitar ta lissafa mutane takwas masu sunayen ‘yan Najeriya da wasu ‘yan ƙasashe daban-daban su huɗu.
Sun haɗa da “Stanley Udeh, mai shekara 46, na Brampton; Odewale Abraham, 57; Oluyemi Sodade, 51; Tosin Damilola Oyebade, 45; Oluwaseyi Olawale Bameke, 39; da Olushola Oke, 42, duk na Toronto.”
Sauran su ne “Gbolahan Qudus Babatunde, mai shekara 29, na Vaughan; Karamveer Singh, 26, na Brampton; Henrik Gancz, 57; Kenneth Okafor, 58; Jaspreet Singh, 25, waɗanda duk aka bayyana ba su da tabbataccen adireshi; da Darryl Davance, 25, na Saint-Jerome, Quebec.”
Waɗanda ake zargin suna fuskantar tuhume-tuhume daban-daban, ciki har da mallakar kadarorin da aka samu ta hanyar aikata laifi, da fataucin kayan sata da darajar su ta wuce dala 5,000, da jabu, da amfani da takardun jabu. Ɗaya daga cikin su kuma yana fuskantar tuhumar tuƙa mota ta hanyar da ke da haɗari.
Rundunar ‘yan sandan yankin Peel ta ce an tuhumi tara daga cikin waɗanda ake zargin aka sake su tare da ranakun zuwa kotu nan gaba, yayin da uku aka tsare su domin sauraron buƙatar beli, daga bisani aka sake su.
‘Yan sandan sun ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin na iya fuskantar matakin hukumar kula da shige da fice, ciki har da yiwuwar korar su daga Kanada, bayan kammala shari’o’in su na laifuka.
Da yake tsokaci kan binciken, Mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Peel, Nick Milinovich, ya ce satar motoci ta hanyar haɗin baki na da alaƙa da wasu manyan laifuka.
“Satar motoci ta hanyar haɗin baki wata harka ce ta cutarwa da ƙungiyoyin masu laifi na ƙasa-da-ƙasa ke gudanarwa, waɗanda ke razana iyalai kuma su ne ke aikata wasu manyan ayyukan laifi. Ta hanyar Project Cadetta, Ofishin mu na Binciken Laifukan Motoci na Kasuwanci tare da abokan aikin mu sun wargaza wannan tsarin daga ɓarayin titi har zuwa dillalan fitar da kaya na ƙasa-da-ƙasa. Mun riga mun rage satar motoci a Peel da fiye da kashi 50 cikin 100 tun lokacin da ta kai ƙololuwa a 2023, kuma ba za mu sassauta ba — babu wurin ɓuya a Peel ga masu aikata laifuka ta hanyar haɗin baki.”
Babban Lauyan Ontario (Solicitor General), Michael Kerzner, ya ce wannan aiki ya nuna jajircewar gwamnati wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
“Satar motoci ta hanyar haɗin baki babban laifi ne da ke barazana ga tsaro da lafiyar al’ummomin mu, kuma gwamnatin mu ba za ta ja da baya ba wajen tunkarar ƙungiyoyin masu aikata laifin da ke da alhaki. Project Cadetta wata shaida ce ta kyakkyawan aikin da Rundunar ‘Yan Sandan Peel da abokan aikin ta ke yi na wargaza waɗannan sarƙaƙƙun ayyuka da hukunta masu laifi. Ta hanyar zuba jari irin su Tallafin Hana Satar Motoci, muna tabbatar da cewa ‘yan sanda suna da kayan aiki da albarkatun da suke buƙata domin daƙile laifuka na haɗin baki, da ƙwato motocin da aka sace, da kare iyalan Ontario.”
Muƙaddashin Daraktan Yanki na Hukumar CBSA a Babban Yankin Toronto, Trishann Pascal, ya ce hukumar ta taimaka wajen hana motocin da aka sace isa kasuwannin ƙasashen waje.
“Jami’an CBSA suna taka muhimmiyar rawa wajen hana motocin da aka sace isa kasuwannin ƙasashen waje ta hanyar duba kwantena da aka zaɓa da kuma miƙa rahotanni. CBSA na taimakawa wajen wargaza ƙungiyoyin masu laifi ta hanyar haɗa bayanan sirri, ƙwarewa, da ayyukan haɗin gwiwa da abokan aikin tabbatar da doka. Wannan bincike ya nuna tasirin wannan haɗin gwiwa.”
Rundunar ‘Yan Sandan Peel ta ce binciken yana ci gaba, kuma ana sa ran ƙarin tuhume-tuhume. Ta kuma bayyana cewa an bayar da sammacin kama ƙarin wasu mutane.
‘Yan sandan sun ce satar motoci a yankin Peel ta ragu da fiye da kashi 50 cikin 100 tun bayan ƙololuwar ta a 2023, tare da ƙarin raguwar kashi 10 cikin 100 a tsawon shekarar 2026 zuwa yanzu.
Wasu daga cikin motocin da aka ƙwato. HOTO: Rundunar ‘Yan Sandan Peel






