Rahoton Sashen Bincike na Majalisar Dokokin Amurka da aka fitar a wannan makon ya ce sojojin Amurka sun yi asarar jiragen sama 81 ko kuma sun samu lalacewa a yaƙin da suke yi da Iran.
Gidan talbijin na CNN ya ruwaito cewa wannan adadin ya haɗa da jiragen sama, jirage masu saukar ungulu da kuma jirage marasa matuƙa. Jirgin MQ-9 Reaper, wanda ake amfani da shi wajen tattara bayanan sirri, sa ido da bincike, tallafa wa sojoji a fagen daga da kuma ayyukan ceto, shi ne ya fi yawan asarar, inda ya ɗauki fiye da rabin adadin jiragen da aka rasa.
Sai dai jerin jiragen da suka lalace ko suka salwanta ya kuma ƙunshi wasu daga cikin muhimman jiragen da Ma’aikatar Tsaron Amurka ke alfahari da su, ciki har da jirgin yaƙi samfurin F-35A da kuma samfurin E-3 Sentry, wani jirgin sama mai injina huɗu da ke ɗauke da wata babbar na’urar hango samaniya (radar) a saman jikin sa, wadda ake amfani da ita wajen gano wuraren da ake kai wa hari da kuma kula da sararin samaniya.
Rahoton ya ce jimillar kuɗin jiragen da aka rasa ko suka lalace na tsakanin dala biliyan 1.9 zuwa dala biliyan 3.3 ne, ya danganta da shirin Ma’aikatar Tsaron Amurka na maye gurbin jiragen. CNN ya ce rahoton ya dogara ne da alƙaluman Ofishin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokokin Amurka.
Sai dai jimillar kuɗin yaƙin ya fi haka nesa ba kusa ba — majiyoyi sun shaida wa CNN cewa ya kai aƙalla dala biliyan 45. Wannan adadi bai haɗa da ɓarnar da aka yi wa ababen more rayuwa a sansanonin sojin Amurka da ke yankin ba, ciki har da sansanonin da wasu daga cikin jiragen suka lalace.
Wasu daga cikin jiragen da aka lissafa a matsayin waɗanda suka yi asara na iya kasancewa an gyara su kuma an mayar da su aiki. Daga cikin su akwai jiragen yaƙi samfurin F-15 Strike Eagle guda takwas, waɗanda suka samu ƙananan lahani sakamakon wani harin Iran da aka kai kan sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti da ke ƙasar Jordan a watan Satumba.
Rahoton ya dogara ne kan alƙaluman da aka samu daga bayanan Ma’aikatar Tsaron Amurka, babban sufeton ma’aikatar, Babbar Rundunar Sojin Amurka (US Central Command), wadda ke gudanar da ayyukan soji kan Iran, da kuma rahotannin kafafen yaɗa labarai da Sashen Bincike na Majalisar Dokokin Amurka ya duba.
Rahoton ya gabatar da wasu tambayoyi da Majalisar Dokokin Amurka ya kamata ta yi la’akari da su, ciki har da ko ‘yan majalisar na samun isassun bayanai daga Ma’aikatar Tsaro kan asarar jiragen, domin su iya tantance illolin da aka samu da kuma hanyoyin magance su.
Ya zuwa yanzu, bayanan Ma’aikatar Tsaron Amurka kan asarar da aka yi a yaƙin Iran ba su fayyace adadin asarar dalla-dalla ba. Haka kuma, rahoton babban sufeton Ma’aikatar Tsaro kan asarar, wanda aka fitar a watan Satumba kuma ya shafi ayyukan da aka gudanar daga ranar 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni, ya yi amfani da wasu alƙaluman asarar jiragen da aka samu daga rahotannin baya na Sashen Bincike na Majalisar Dokokin Amurka.
A cewar CNN, wasu batutuwan da Majalisar Dokokin Amurka ke buƙatar yin nazari a kan su sun haɗa da ko za ta ware kuɗaɗe domin gyara ko maye gurbin jiragen da suka lalace ko suka salwanta; ko masana’antun cikin gida suna da isasshen ƙarfin samar da jiragen da ake buƙata; da kuma irin tasirin da yaƙin zai iya yi kan sayar da makamai da kayan aikin soji na Amurka ga ƙasashe abokai.
Rahoton ya kuma yi tambaya kan yadda yaƙin Iran ya shafi matsayin sojin Amurka a wajen yankin Gabas ta Tsakiya.






