Musulmi za su kasance mafi yawan mabiya addini a duniya, inda za su zarce Kiristoci nan da shekarar 2035, duk da cewa ana sa ran mabiya addinan biyu za su ci gaba da ƙaruwa, a cewar wani sabon hasashe na Cibiyar Bincike ta Pew (Pew Research Center) da ke Amurka.
Hasashen ya nuna cewa Musulunci zai fi Kiristanci saurin ƙaruwa a cikin shekaru masu zuwa, musamman saboda yawan haihuwa a tsakanin Musulmi, yayin da sauya addini zai fi shafar raguwar ƙaruwa a yawan Kiristoci.
A cewar rahoton wanda Conrad Hackett ya rubuta, tsakanin shekarar 2020 da 2025, kowace mace Musulma ta haifi yara 3.1 a matsakaicin hasashe, idan aka kwatanta da yara 2.5 ga kowace mace Kirista da kuma yara 1.6 ga mata masu sauran addinai.
Rahoton ya ce ana sa ran Musulmi da Kiristoci za su ci gaba da samun ƙarin mutane ta hanyar haihuwa fiye da waɗanda suke rasuwa, lamarin da masana ƙididdigar al’umma ke kira “natural population change”, wato bambancin yawan haihuwa da mutuwa.
Tsakanin shekarun 2020 da 2070, ana hasashen yawan Musulmi zai ƙaru da mutane biliyan 1.6 sakamakon wannan bambanci, yayin da Kiristoci za su ƙaru da mutane miliyan 792.
Sauya addini ma zai taka rawa wajen sauyin yawan mabiya addinan biyu, duk da cewa tasirin sa zai kasance ƙasa da na haihuwa da mutuwa.
Rahoton ya ƙiyasta cewa Musulunci zai yi asarar mutane miliyan takwas ta hanyar sauya addini, yayin da Kiristanci zai yi asarar kusan mutane miliyan 105, waɗanda mafi yawan su ake sa ran za su koma cikin waɗanda ba sa danganta kan su da wani addini.
Sai dai ana hasashen sauya addini tsakanin Kiristanci da Musulunci zai kusan daidaita, inda mutane miliyan 9.2 za su sauya daga Musulunci zuwa Kiristanci, yayin da mutane miliyan tara za su sauya daga Kiristanci zuwa Musulunci.
Hasashen ya nuna cewa ƙaruwa a yawan Musulmi ba zai kasance sakamakon waɗanda ke barin Kiristanci su koma Musulunci ba, sai dai galibi saboda wasu dalilai na ƙididdigar al’umma, musamman yawan haihuwa.
A matakin ƙasashe, ana sa ran mafi yawan ƙaruwa a yawan Musulmi zai faru ne a ƙasashen da Musulmi suka riga suka fi yawa.
A shekarar 2020, Musulmi sun fi yawa a ƙasashe 53, kuma ana hasashen waɗannan ƙasashe za su ƙara samun Musulmi biliyan 1.2 zuwa shekarar 2070, wanda zai wakilci kashi 74 cikin 100 na ƙarin Musulmi da ake sa ran za a samu a duniya.
Ƙasar Pakistan, wadda a shekarar 2020 take da al’ummar Musulmi ta biyu mafi girma a duniya, ana hasashen za ta zama ƙasar da ta fi kowace yawan Musulmi nan da 2070, inda adadin Musulman ƙasar zai tashi daga miliyan 227 zuwa miliyan 461.
Haka kuma, ana sa ran ƙaruwa a yawan Kiristoci zai fi yawa a ƙasashen da Kiristoci suka riga suka fi yawa.
Ƙasashe 120 da Kiristoci suka fi yawa a cikin su a shekarar 2020, ana hasashen za su ƙara samun Kiristoci miliyan 630 zuwa shekarar 2070, wanda zai wakilci kashi 92 cikin 100 na ƙarin Kiristocin da ake hasashen za a samu a duniya.
Jamhuriyar Dimokiraɗiyyar Kongo na daga cikin ƙasashen da ake hasashen za su samu babbar ƙaruwa, inda adadin Kiristocin ƙasar zai tashi daga miliyan 92 a shekarar 2020 zuwa miliyan 299 a shekarar 2070.
Sai dai ana sa ran wasu ƙasashe da Kiristoci suka fi yawa za su samu raguwar Kiristoci saboda sauya addini da kuma tsufa a cikin al’umma, wanda zai iya sa yawan mace-mace ya zarce haihuwa.
Amurka, wadda a shekarar 2020 take da mafi yawan Kiristoci a duniya, ana hasashen za ta samu mafi girman raguwar Kiristoci, inda adadin su zai ragu daga miliyan 217 zuwa miliyan 174 nan da shekarar 2070.
A matakin yankuna, ana hasashen Musulmi za su kasance ƙungiyar addini mafi ƙanƙanta a yawancin yankunan duniya, duk da saurin ƙaruwa da suke samu.
Nan da shekarar 2070, ana hasashen Musulmi za su kasance kashi 95 cikin 100 na al’ummar yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, inda suka daɗe suna rinjaye.
Yankin Asiya da Pasific ne ake hasashen zai kasance yanki guda da za a samu sauyin ƙungiyar addini mafi rinjaye, inda Musulmi za su zarce waɗanda ba sa danganta kan su da wani addini.
A gefe guda, ana hasashen Kiristoci za su ci gaba da kasancewa mafi yawan mabiya addini a yawancin yankuna, duk da cewa kaso na Kiristoci a cikin al’ummar yankunan zai ragu a duk duniya, ban da yankin Asiya da Pasific, inda ake sa ran zai kasance kusan yadda yake idan abubuwan da ake gani a yanzu suka ci gaba.
Rahoton ya bayyana cewa raguwar kaso na Kiristoci a cikin al’ummar wani yanki ba lallai ba ne ya nuna cewa adadin Kiristocin ya ragu.
Misali, a yankin Afirka Kudu da Sahara, ana hasashen yawan Kiristoci zai ƙaru da kashi 129 cikin 100 tsakanin 2020 da 2070, yayin da yawan Musulmi zai ƙaru da kashi 166 cikin 100. Wannan na nufin Kiristoci za su ƙaru a adadi, amma kaso nasu a cikin jimillar al’ummar yankin zai ragu saboda Musulmi za su ƙaru da sauri.
Rahoton mai taken “Islam Will Soon Be the World’s Largest Religion, but Christianity Will Keep Growing Too” (Musulunci Zai Zama Addini Mafi Yawan Mabiya a Duniya Nan Ba Da Daɗewa Ba, Amma Kiristanci Ma Zai Ci Gaba da Ƙaruwa) Cibiyar Bincike ta Pew ta wallafa shi a ranar 18 ga Nuwamba, 2026.
Conrad Hackett ne ya rubuta rahoton, wanda ya yi nazari kan sauye-sauyen yawan al’umma, yawan haihuwa, sauya addini da kuma yanayin ƙaruwa ko raguwa a yankuna daban-daban na duniya, waɗanda ke tasiri ga makomar Musulunci da Kiristanci.






