Isra’ila da Amurka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya wadda za ta bai wa Amurka wani fili a Yammacin Ƙudus da Falasɗinawa suka mallaka kafin shekarar 1948, domin ya zama wurin dindindin na sabon Ofishin Jakadancin Amurka a birnin.
“Yarjejeniyar hayar filin na tsawon shekaru 99 ce, kuma Amurka za ta biya Isra’ila dala 1 kacal,” inji Jakaden Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee.
A wa’adin sa na farko a watan Disamba 2017, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ba da umurnin mayar da Ofishin Jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Birnin Ƙudus.
Wannan mataki ya fuskanci suka daga ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa a wancan lokaci, saboda ana kallon sa a matsayin saɓa wa matsayar ƙasa da ƙasa kan matsayin birnin Ƙudus.
Duk da mayar da Ofishin Jakadancin Amurka, yawancin ƙasashe har yanzu suna ci gaba da ajiye ofisoshin jakadancin su ne a Tel Aviv.
A shekarar 2022, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Adalah da ke Isra’ila ta bayyana cewa filin da aka ware domin gina harabar ofishin jakadancin an ƙwace shi ne daga hannun Falasɗinawa bisa Dokar Kadarorin Waɗanda Ba Su Nan ta Isra’ila ta shekarar 1950.
Adalah ta ce faɗaɗa harabar Ofishin Jakadancin Amurka a Yammacin Ƙudus da kuma ƙwace filin da aka ware domin hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, musamman Mataki na 46 na Dokokin Hague, wanda ya haramta ƙwace kadarorin masu zaman kan su.
(Fassara daga shafin TR World)






