• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Katsina 2027: Ɗanmarke ya naɗa tsohon kakakin soji Sagir Musa daraktan yaƙin neman zaɓe

* Ya ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓe masu mambobi sama da 2,000, ya yi alƙawarin inganta tsaro da samar da kiwon lafiya kyauta

UMAR GARBA by UMAR GARBA
November 17, 2026
in Siyasa
A A
0
Katsina 2027: Ɗanmarke ya naɗa tsohon kakakin soji Sagir Musa daraktan yaƙin neman zaɓe
Daga hagu: Sanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarke da Birgediya Janar Sagir Musa (ritaya)

Daga hagu: Sanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarke da Birgediya Janar Sagir Musa (ritaya)

Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Sanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarke, ya naɗa tsohon kakakin Rundunar Sojin Nijeriya, Birgediya Janar Sagir Musa (ritaya) a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen sa a zaɓen 2027.

An ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen tare da wasu kwamitoci guda 17, waɗanda suka ƙunshi ƙwararru, ‘yan siyasa da masu sa kai sama da 2,000.

Za su kula da harkokin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Bikin ƙaddamarwar, wanda aka gudanar a hedikwatar PDP ta jihar da ke birnin Katsina, ya samu halartar ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki.

Da yake jawabi a wajen taron, Ɗanmarke ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ƙoƙari na ƙarfafa tsarin gudanarwar jam’iyyar da faɗaɗa hulɗa da al’umma.

Ya ce naɗin Sagir Musa zai taimaka wajen daidaita ayyukan kwamitocin da tabbatar da ingantaccen tsarin aiwatar da manufofin jam’iyyar a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ɗanmarke, wanda tsohon ɗan Majalisar Tarayya kuma ɗan kasuwa ne, ya bayyana tsaro, kiwon lafiya, riƙon amana da kula da dukiyar jama’a a matsayin manyan abubuwan da zai mayar da hankali a kai idan ya zama gwamna.

Ya yi alƙawarin magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi jihar, inganta riƙon amana a gwamnati da kuma samar da magani kyauta a asibitocin gwamnati idan aka zaɓe shi.

An haifi Ɗanmarke a shekarar 1961 a Ɗanmarke, Jihar Katsina. Ya fara harkokin sa a fannin kasuwanci kafin ya shiga siyasa bayan dawowar Nijeriya tsarin dimokiraɗiyya a 1999.

Ya fara siyasa a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara daga 1999 zuwa 2002. A 2003, an zaɓe shi a Majalisar Wakilai ta Tarayya, inda ya yi aiki har zuwa 2007. Daga bisani, ya zama Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu.

Tarihin Sagir Musa a Rundunar Soji

Shi kuwa Sagir Musa, tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ne ya naɗa shi matsayin kakakin Rundunar Sojin Nijeriya a watan Fabrairun 2019, lokacin da yake matsayin Kanal.

Ya maye gurbin Birgediya Janar Sani Usman Kukasheƙa (mai ritaya), wanda ya taɓa zama Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Ƙasa.

Kafin naɗin sa, Sagir ya yi aiki a matsayin kakakin runduna ta 82 ta Sojin Nijeriya da ke Inugu, inda ya kula da harkokin sadarwa da kafafen yaɗa labarai.

A ranar 25 ga Nuwamba, 2020, Majalisar Soji ta amince da ɗaga shi zuwa matsayin Birgediya Janar tare da wasu manyan hafsoshin soja 135.

A lokacin aikin sa, Sagir ya samu ƙwarewa a fannin sadarwar soji, hulɗa da kafafen yaɗa labarai, kula da bayanai da kuma yaɗa bayanan da suka shafi ayyukan soji da tsaron ƙasa.

Ana sa ran wannan ƙwarewa za ta taimaka masa wajen jagorantar harkokin sadarwa, hulɗa da masu ruwa da tsaki da kuma ayyukan gudanarwa na majalisar yaƙin neman zaɓen PDP.

PDP Ta Yi Bayanin Tsarin Yaƙin Neman Zaɓe

A nasa jawabin, Shugaban PDP na Jihar Katsina, Honourable Nura Amadi Kurfi, ya ce ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen na nuna irin shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi domin zaɓen gwamna na 2027.

Ya bayyana cewa mambobin kwamitocin sun fito daga fannoni daban-daban, ciki har da ‘yan kasuwa, masana’antu, tsoffin ma’aikatan gwamnati, tsofaffin jami’an tsaro, ɗalibai, mata da wakilan ƙungiyoyi masu muradu daban-daban.

A cewar sa, haɗa mutane masu irin wannan bambancin ƙwarewa zai taimaka wajen isar da saƙonnin jam’iyyar ga al’ummomi daban-daban.

Kurfi ya buƙaci mambobin kwamitocin da su kasance masu jajircewa, ladabi da haɗin kai wajen gudanar da ayyukan su. Ya kuma jaddada muhimmancin kai manufofin jam’iyyar kai-tsaye ga masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Ya tabbatar da cewa a shirye PDP take ta shiga zaɓen gwamnan na 2027, tare da bayyana tabbacin nasarar shirye-shiryen jam’iyyar.

Ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen na nuna wani sabon mataki a shirye-shiryen Ɗanmarke na neman kujerar gwamnan Katsina, inda ake sa ran Sagir Musa da sauran mambobin za su jagoranci tattara magoya baya, hulɗa da al’umma da kuma yaɗa manufofin jam’iyyar a faɗin jihar.

Tare da rahoton PRNigeria

Tags: Birgediya Janar Sagir Musa (ritaya)KatsinaPDPSanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarkezaben2027
Previous Post

An kama ‘yan Najeriya takwas a Kanada kan satar motoci na dala miliyan 4.5

Next Post

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!