• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Minista Idris ya yi jimamin rasuwar Shugaban Hukumar Ƙidaya, Aminu Wushishi

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
August 28, 2026
in Labarai
A A
0
Minista Idris ya yi jimamin rasuwar Shugaban Hukumar Ƙidaya, Aminu Wushishi
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris (a hagu), tare da marigayi Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Alhaji Aminu Wushishi, lokacin wata ziyara a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris (a hagu), tare da marigayi Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Alhaji Aminu Wushishi, lokacin wata ziyara a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, tare da marigayi Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Alhaji Aminu Wushishi, lokacin wata ziyara a Abuja

Minista Idris ya yi jimamin rasuwar Shugaban Hukumar Ƙidaya, Aminu Wushishi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaduwa da alhini kan rasuwar Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Kasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf Wushishi, Talban Wushishi.

A cikin wata sanarwa da Mataimakin sa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim, ya fitar, Ministan ya ce: “Na samu labarin rasuwar Dakta Aminu Yusuf Wushishi cikin tsananin baƙin ciki. Rasuwar sa babban rashi ne ga Hukumar Kidaya ta Kasa, ma’aikatan gwamnati da ƙasa baki ɗaya.”

Marigayi Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Dakta Aminu Wushishi

Idris ya bayyana marigayin a matsayin abokin sa na ƙut-da-ƙut kuma ma’aikacin gwamnati mai kishin ƙasa, wanda jajircewar sa wajen cigaban ƙasa ta bayyana a cikin ɗan gajeren lokacin da ya yi a hukumar.

Ya ce Dakta Wushishi ya fara aikin sa da kyakkyawar manufa ta gudanar da sahihiyar ƙidayar jama’a da gidaje wadda za a yi amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ita, domin samar da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin ƙasa.

Ya ce wannan batu na daga cikin muhimman abubuwan da ya sanya a gaba tun bayan kama aikin sa.

“Shirin sa da jajircewar sa na gudanar da sahihiyar ƙidayar jama’a da za a yi amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ita, sun nuna irin nauyin da yake ji na alhakin ƙasa da kuma ƙudirin da yake da shi na barin gagarumar gudunmawa mai ɗorewa ga ci gaban Najeriya,” inji shi.

Idris ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Neja, da kuma ɗaukacin al’ummar Wushishi, inda marigayin ya riƙe babbar sarautar gargajiya ta Talban Wushishi.

Ministan ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin, abokan aikin sa, abokan sa da ma’aikatan Hukumar Ƙidaya ta Kasa, yana addu’ar Allah ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi.

Ya roƙi Allah ya gafarta wa marigayin kurakuran sa, ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, sannan ya ba duk waɗanda ke alhinin rasuwar sa haƙurin jure wannan babban rashi.

Tags: Dakta Aminu Yusuf WushishiHukumar Ƙidaya ta Kasa (NPC)Mohammed Idrista'aziyyaTalban Wushishi.
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta goyi bayan tsarin cigaban Taraba, ta yi alƙawarin ƙarfafa haɗin gwiwa

Next Post

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!