• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Nasarorin tattalin arziki: ‘Yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje sun aiko da dala miliyan 947 a Yuli – CBN

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
August 30, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira
Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa a cikin watan Juli na 2026, Nijeriya ta samu kuɗaɗen da ’yan ƙasar mazauna ƙasashen waje suka turo cikin ƙasa waɗanda adadin su ya kai dala miliyan 947.

CBN ya ce an turo jimillar adadin waɗannan kuɗi ne ta hannun kamfanonin aika kuɗi na ƙasa da ƙasa (IMTOs) a watan Yuli 2026.

Wannan shi ne mafi yawan kuɗaɗen da aka taɓa samu a cikin wata guda ta hanyoyin da aka amince da su, kuma hakan ya ƙara kusantar da Babban Bankin Nijeriya (CBN) a ƙoƙarin bankin na ganin ya cimma burin sa na samun dala biliyan ɗaya a duk wata.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa kuɗaɗen da aka shigo da su ta hannun IMTOs sun kai dala biliyan 3.8 a cikin watanni bakwai na farkon shekarar 2026, wanda ke nuna ƙarin kashi 50.2 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a makamancin wannan lokaci na shekarar 2025.

Haka kuma sabbin alƙaluman sun nuna gagarumin ƙaruwa a yawan kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke turawa cikin ƙasar ta hanyoyin kuɗi na hukuma, yayin da CBN ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi inganta gaskiya, sauƙaƙa hanyoyin aika kuɗi da kuma ƙara gasa a kasuwar aiko kuɗaɗen ƙasashen waje zuwa Nijeriya.

Waɗannan sauye-sauyen sun haɗa da matsawa zuwa tsarin canjin kuɗin waje da kasuwa ke ƙayyadewa, sauya dokokin da ke kula da ayyukan kamfanonin IMTOs, da kuma ƙaddamar da Lambar Tabbatar da Bankin ’Yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje (NRBVN).

CBN ya kuma ƙara ƙarfafa hulɗa da kamfanonin IMTOs, bankuna da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, tare da ƙarfafa buƙatar tabbatar da cewa duk wasu hadahadar aika kuɗaɗen ƙasashen waje su ratsa ta asusun ajiyar kuɗaɗen da aka ware na musamman a bankunan dillalan kuɗin waje da aka bai wa izini.

A cewar CBN, ƙarin kuɗaɗen da ake samu ta hanyoyin hukuma na da muhimmiyar fa’ida fiye da samun wani babban adadi a cikin wata guda kawai. Ƙarin kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke turawa na iya taimakawa wajen ƙara yawan kuɗaɗen waje da ke samuwa a kasuwa, inganta gaskiya a harkar musayar kuɗi, tare da tallafa wa amfani da kuɗi a gidaje, saka hannun jari da kuma ganin Nijeriya na samun kuɗaɗen waje daga ƙetare.

“Lokacin da muka tsara cimma wani buri bayyananne na kai yawan kuɗaɗen da ake turo wa Nijeriya ta hanyoyin hukuma zuwa dala biliyan ɗaya a kowane wata, kusan shekaru biyu da suka wuce, wasu mutane sun yi tunanin cewa mafarki muke yi. Yanzu da muka samu dala miliyan 947 a watan Yuli, mun kusa cimma wannan buri,” inji Cardoso.

Gwamnan ya ce manufar CBN ba ta tsaya kawai wajen samun wani babban adadi a cikin wata guda ba, sai dai tabbatar da cewa ana ci gaba da samun ƙaruwa mai ɗorewa a yawan kuɗaɗen da ake turowa cikin Nijeriya ta hanyoyin hukuma.

CBN ya ce ƙarin da aka samu cikin watanni bakwai na farko na shekarar 2026 ya samo asali ne daga tasirin matakan da aka ɗauka domin sanya hanyoyin aiko kuɗaɗen ƙasashen waje na hukuma su kasance masu sauƙin amfani, gasa da kuma gaskiya.

CBN ya ce zai ci gaba da tabbatar da ɗorewar wannan nasara ta hanyar ƙara hulɗa da al’ummomin ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da masu ruwa da tsaki a harkar kuɗi a manyan hanyoyin da ake tura kuɗaɗe zuwa Nijeriya.

A wani ɓangare na hulɗar da yake yi a ƙasashen waje, CBN ya ce zai ci gaba da amfani da damar da yake samu a manyan cibiyoyin hadahadar kuɗi na duniya domin tattaunawa da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, kamfanonin IMTOs, bankuna da sauran masu ruwa da tsaki, da nufin rage matsalolin da ke kawo cikas ga aika kuɗaɗe da kuma ƙarfafa mutane su riƙa amfani da hanyoyin hukuma wajen tura kuɗi.

“Adadin miliyoyin dalolin da mazauna ƙasashen waje suka aiko Nijeriya a cikin watan Yuli wata muhimmiyar alama ce, amma abin da muka fi mayar da hankali a kai ba nasarar wata guda ɗaya ba ce. Abin da muke so shi ne samar da yanayin da zai bada damar ci gaba da samun ƙaruwa mai ɗorewa a kuɗaɗen da ake turo wa Nijeriya ta hanyoyin hukuma. Muna sa ran ci gaba da ganin kyautatuwa, kuma mun yi imanin cewa Nijeriya za ta iya cimma, sannan ta ci gaba da samun, sama da dala biliyan ɗaya a duk wata,” cewar Cardoso.

Tags: CBNOlayemi Cardoso
Previous Post

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da gangamin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da gangamin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da gangamin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!