• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kiwon Lafiya

Gwamna Bago ya ƙaddamar da kayan aikin asibiti na Naira miliyan 100 domin inganta harkar lafiya a Neja

Admin-content by Admin-content
August 19, 2026
in Kiwon Lafiya
A A
0
Gwamna Bago ya ƙaddamar da kayan aikin asibiti na Naira miliyan 100 domin inganta harkar lafiya a Neja
Kwamishinan Lafiya na Jihar Neja, Dakta Muhammad Murtala Bagana, yana jawabi a madadin Gwamna Mohammed Umaru Bago a wajen ƙaddamar da kayan aiki, magunguna da sauran kayayyaki a Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida

Kwamishinan Lafiya na Jihar Neja, Dakta Muhammad Murtala Bagana, yana jawabi a madadin Gwamna Mohammed Umaru Bago a wajen ƙaddamar da kayan aiki, magunguna da sauran kayayyaki a Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida

Gwamnatin Jihar Neja ta ƙaddamar da kayan aikin asibiti, magunguna da sauran kayayyaki da darajar su ta kai Naira miliyan 100 a Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida, a wani mataki na ƙarfafa harkokin kiwon lafiya a faɗin jihar.

An samar da kayan aikin ne tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya, kuma ana sa ran za su ƙara wa asibitin ƙarfin samar da ingantaccen kiwon lafiya cikin lokaci, musamman wajen kula da mata masu juna biyu da jarirai, ga al’ummar da ke ƙarƙashin kulawar asibitin.

Da yake ƙaddamar da kayan a madadin Gwamna Mohammed Umaru Bago, Kwamishinan Lafiya, Dakta Muhammad Murtala Bagana, ya ce wannan tallafi ya nuna ƙudirin gwamnatin jihar na inganta ayyukan kiwon lafiya da tabbatar da cewa asibitocin gwamnati suna da isassun kayan aiki.

Bagana ya ce samar da kayan aikin yana daga cikin manyan jarin da jihar ke yi wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ta, kuma zai taimaka wa asibitin wajen mayar da martani yadda ya kamata ga buƙatun lafiyar al’ummar da ke ƙaruwa.

A cewar sa, Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida yana cikin manyan asibitoci 22 da aka ware domin gyarawa karkashin shirin bunƙasa harkar kiwon lafiya na gwamnatin jihar.

Ya ce sauran asibitocin da aka ware domin irin wannan aiki sun hada da waɗanda ke Kontagora, New Bussa da Sabon Wuse, da sauran su.

Magunguna da sauran kayayyaki da darajar su ta kai Naira miliyan 100 da aka ƙaddamar a Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida

Kwamishinan ya ce wannan tallafi yana daga cikin ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan Cikakken Kula da Matsalolin Haihuwa na Gaggawa da Jarirai (CEmONC), ciki har da inganta Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, dukkan su a Bida.

Ya ce manufar ita ce taimakawa wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai da za a iya kauce musu a jihar.

Bagana ya bayyana cewa cibiyoyin kiwon lafiyar da ke Bida suna hidima ga al’ummomin Bida, Agaie, Katcha, Gbako, Edati da Lavun, da kuma wasu al’ummomin jihohin maƙwabta.

Ya ce ana sa ran ayyukan za su amfani al’ummar da ke ƙarƙashin kulawar cibiyoyin, waɗanda yawan su ya kusan mutum miliyan biyu, ciki har da mata kimanin 400,000 da ke shekarun haihuwa.

Kwamishinan ya ce ƙara ƙarfin Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da Babban Asibitin Bida zai ƙarfafa gwiwar mata wajen neman kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya da kuma haihuwa a asibitoci, tare da rage jinkirin da ke faruwa yayin tura marasa lafiya daga wannan asibiti zuwa wani.

A cewar Bagana, Gwamna Bago ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na tallafa wa ayyukan Gwamnatin Tarayya ta hanyar zuba jari a harkokin tafiyar da kiwon lafiya, bunƙasa ma’aikatan lafiya, kula da cibiyoyin kiwon lafiya da kuma tabbatar da samun muhimman magunguna da kayayyakin asibiti a kowane lokaci.

Ya ce ƙoƙarin jihar na bunƙasa harkar kiwon lafiya ya yi daidai da manyan manufofin Nigeria Health Sector Renewal Investment Initiative da kuma National Health Compact na Gwamnatin Tarayya.

Bago ya ce Jihar Neja na ƙarfafa cibiyoyin ta da asibitocin ta domin taimakawa wajen gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya na ƙasa wanda zai iya fuskantar ƙalubale yadda ya kamata.

Ya jaddada muhimmancin samar da kayayyakin aiki na musamman ga asibitocin gwamnati domin inganta sakamakon jinya da kuma dawo da amincewar jama’a ga asibitocin gwamnati.

Masarautar ta yaba da wannan tallafi, inda Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja, Alhaji Dakta Yahaya Abubakar, ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa ƙoƙarin ta na inganta harkar kiwon lafiya.

Sarkin ya ce ƙarin kayan aiki da kayayyakin asibitin zai taimaka matuƙa wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a Bida da sauran al’ummomin da ke kewaye.

Ya buƙaci mahukuntan asibitin da su tabbatar da cewa an yi amfani da kayan aikin yadda ya kamata tare da kula da su domin amfanin al’umma.

Etsu Nupe ya kuma buƙaci mazauna yankin, musamman mata masu juna biyu, da su riƙa zuwa duba lafiyar su a kai a kai tare da amfani da asibitocin gwamnati domin samun haihuwa cikin aminci ƙarƙashin kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Neja, Dakta Abdullahi Usman Imam; Shugaban Sashen Ayyukan Asibiti na Babban Asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida, Dakta Mohammed Imam; da Shugaban Ƙaramar Hukumar Bida, Muhammad Manko Usman, su ma sun yaba da wannan tallafi.

Sun yaba wa gwamnatin jihar da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya bisa ci gaba da haɗin gwiwar su wajen inganta harkar kiwon lafiya a Jihar Neja.

Ana sa ran tallafin Naira miliyan 100 zai taimaka wajen cika giɓin da ke akwai tare da shirin gyaran manyan asibitoci 22, faɗaɗa ayyukan kula da matsalolin haihuwa da jarirai na gaggawa, bunƙasa ma’aikatan lafiya da kuma tabbatar da samar da muhimman magunguna da kayayyakin asibiti a faɗin jihar.

Ga mazauna Bida da yankunan da ke kewaye, ana sa ran wannan tallafi zai inganta damar samun kiwon lafiya, ƙarfafa ayyukan gaggawa, inganta kula da mata masu juna biyu da jarirai, tare da rage cunkoso a cibiyoyin da ake tura marasa lafiya zuwa gare su.

Sai dai gwamnatin jihar tana fuskantar ƙalubalen tabbatar da cewa sababbin kayan aikin sun ci gaba da aiki yadda ya kamata ta hanyar kula da su, samar da isassun ma’aikatan lafiya da tabbatar da wadatar magunguna da sauran kayayyakin asibiti.

Wannan tallafi yana daga cikin babban shirin gwamnatin Bago na bunƙasa harkar kiwon lafiya, wanda ya mayar da hankali kan inganta gine-ginen asibitoci da ayyukan kiwon lafiya a matsayin muhimman ginshiƙan bunƙasa ɗan’adam da inganta rayuwar al’ummar Jihar Neja.

Tags: asibitiGwamna Bagokiwon lafiyaNeja
Previous Post

Dillalan mota a Abuja na cikin fargaba yayin da Wike ya haramta amfani da wuraren shuke-shuke da wuraren shaƙatawa a matsayin wajen sayar da motoci

Next Post

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

Related Posts

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su
Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su

July 9, 2026
Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya
Kiwon Lafiya

Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya

June 9, 2026
Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA
Kiwon Lafiya

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

April 20, 2026
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata
Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

April 5, 2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500
Kiwon Lafiya

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500

April 3, 2026
Next Post
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!