Fadar Shugaban Ƙasa ta soki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kan alƙawarin sa na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce wannan alƙawari na Atiku ya nuna sauyin matsaya kan wani muhimmin ɓangare na manufofin tattalin arzikin sa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Onanuga ya ce Atiku ya taɓa nuna goyon bayan sa ga cire tallafin man fetur a lokacin yaƙin neman zaɓen sa na 2023, amma yanzu ya sauya matsayin sa domin neman karɓuwa a wajen masu kaɗa ƙuri’a.
Ya ce dawo da tallafin man fetur ba abu ne mai sauƙi ba, saboda Dokar Masana’antun Man Fetur (Petroleum Industry Act – PIA) ta tanadi kawo ƙarshen tsarin tallafin tun daga ƙarshen watan Yuni 2023.
Onanuga ya bayyana cewa tallafin ba wasu kuɗaɗe ba ne da suke a taskar gwamnati domin raba wa jama’a, sai dai wani tsari ne da gwamnati ke amfani da shi wajen biyan tazarar da ke tsakanin kuɗin da ake sayen man fetur da kuma farashin da ake sayar da shi ga jama’a.
A cewar sa, wannan tsari ya janyo wa gwamnati asarar maƙudan kuɗaɗe a baya, tare da ƙara dogaro da bashi domin ɗaukar nauyin tallafin.
“Idan aka dawo da tallafin, tambayar da ya kamata ‘yan Nijeriya su yi ita ce: wa zai biya kuɗin?” inji shi.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawarar ya ce idan aka sayar da man fetur a ƙasa da ainihin kuɗin da aka kashe wajen samar da shi, dole ne gwamnati ta ɗauki nauyin biyan gibin. Wannan, a cewar sa, na iya rage kuɗaɗen da ake warewa ayyukan more rayuwa da sauran hidimomin jama’a, ko kuma ya ƙara yawan bashin ƙasa.
Ya ce harkar fetur a Nijeriya ta samu sauyi sosai tun bayan cire tallafin, musamman saboda ƙaruwa da ake samu wajen samar da man fetur a cikin gida.
Onanuga ya ce matatar man fetur ta Dangote da sauran matatun cikin gida sun ƙara samar da man fetur, abin da ya taimaka wajen rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.
Ya yi gargaɗin cewa dawo da tsohon tsarin tallafin na iya kawo cikas ga ci gaban matatun cikin gida, tare da rage jarin da ake zubawa a ɓangaren.
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen da gwamnati ta daina kashewa wajen tallafin man fetur sun taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ake rabawa matakan gwamnati uku daga asusun tarayya.
A cewar sa, a watan Yuli kaɗai, gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba kusan Naira tiriliyan uku daga asusun tarayya, wanda ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin sakamakon cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauyen da aka samu a tsarin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje.
Sai dai Onanuga ya amince cewa ƙarin farashin man fetur ya jefa ‘yan Nijeriya da kamfanoni cikin matsin tattalin arziki, musamman sakamakon ƙarin kuɗin sufuri da makamashi.
Ya ce gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin rage wannan matsin ta hanyar ƙarfafa amfani da iskar gas ɗin CNG, wanda gwamnati ta ce zai iya rage kuɗin makamashi sosai idan aka kwatanta da man fetur.
Onanuga ya ce abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai shi ne samar da mafita mai ɗorewa da za ta rage wa ‘yan Nijeriya raɗaɗin tsadar makamashi, maimakon komawa wani tsarin tallafi da ya daɗe yana janyo wa gwamnati matsalolin kuɗi.
Ya buƙaci Atiku da sauran ‘yan siyasar da ke neman dawo da tallafin da su bayyana wa ‘yan Nijeriya cikakken tsarin da za su bi wajen aiwatar da manufar.
Ya ce ya kamata su bayyana nawa shirin zai ci a kowace shekara, daga ina za a samo kuɗaɗen, ko gwamnati za ta sake karɓar bashi domin ɗaukar nauyin tallafin, da kuma yadda za a kare tsarin daga almundahana.
“Alƙawurran siyasa dole ne su kasance tare da lissafin kuɗin da zai tabbatar da ɗorewar su,” in ji Onanuga.
Ya ƙara da cewa muhawarar kan tsadar rayuwa da manufofin tattalin arziki na da muhimmanci, amma ya kamata a gudanar da ita bisa la’akari da halin da tattalin arzikin Nijeriya yake ciki a yanzu, ba bisa tsarin tattalin arzikin man fetur na baya ba.







