• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

CBN ya ɗauki matakan daƙile kaka-gidan kamfanonin fintech, tare da kare haƙƙoƙin masu harkokin kuɗi

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
August 4, 2026
in Labarai
A A
0
CBN ya ɗauki matakan daƙile kaka-gidan kamfanonin fintech, tare da kare haƙƙoƙin masu harkokin kuɗi
CBN da hatimomin wasu kamfanonin 'fintech'

CBN da hatimomin wasu kamfanonin 'fintech'

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa yana ƙaddamar da sababbin ƙa’idoji masu tsauri ga kamfanonin fintech da masu samar da ayyukan biyan kuɗi ta hanyar dijital domin tabbatar da adalci da gasa mai inganci a fannin harkokin kuɗi.

Da yake jawabi a Taron Business Journal Fintech and Financial Inclusion na shekarar 2026 karo na uku da aka gudanar a Legas, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ba za a bari wata cibiyar kuɗi ta mamaye kasuwa ta yadda hakan zai hana gasa ko kuma ya cutar da masu amfani da ayyukan hadahadar kuɗi ba.

Cardoso, wanda Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Dakta Rakiya Opemi Yusuf ta wakilta a taron, ya ce manufar CBN ita ce samar da yanayin da bankuna, kamfanonin fintech da sauran masu samar da ayyukan biyan kuɗi za su yi gasa cikin adalci ƙarƙashin ƙa’idoji bayyanannu tare da kare haƙƙin kwastomomi.

Ya bayyana cewa, duk da cewa ƙirƙire-ƙirƙire na da muhimmanci wajen faɗaɗa shigar jama’a cikin harkokin kuɗi da inganta tsarin biyan kuɗi, bai kamata a yi amfani da shi wajen samun rinjaye na rashin adalci ba.

A cewar Cardoso, CBN ya samar da sabbin ƙa’idojin tsarin kasuwa da nufin rage mamayar da wasu ke yi a fannin ayyukan biyan kuɗi, musamman a ɓangaren fitar da kayan biyan kuɗi ga masu amfani da kuma karɓar kuɗin ‘yan kasuwa.

Ya ce waɗannan matakan za su hana kowace hukuma amfani da ƙarfinta a wani ɓangare na kasuwa domin ta mallaki ko ta rinjayi wani ɓangare cikin rashin adalci.

Cardoso ya jaddada cewa sabuwar manufar ba ta da nufin hana kasuwanci bunƙasa, sai dai tabbatar da cewa ci gaban kasuwanci ba zai rage gasa, zaɓin kwastomomi ko kuma ya kawo barazana ga zaman lafiya da daidaito ga tsarin kuɗin Nijeriya ba.

Haka kuma ya sanar da cewa CBN zai ƙara tabbatar da gaskiya ta hanyar wajabta wa cibiyoyin kuɗi bayyana ainihin waɗanda suka mallake su, domin hana ɓoyayyen tsarin mallaka da kuma rikice-rikicen da ka iya biyo baya.

Daga nan sai ya ce daga yanzu dukkan bayanan mu’amalolin biyan kuɗi da ake samarwa a Nijeriya dole ne a adana su kuma a sarrafa su a cikin Nijeriya.

Ya ce hakan zai ƙarfafa tsaron bayanai, inganta sa-ido na hukumomin kula da harkokin kuɗi, tare da rage dogaro da tsarin adana bayanai na ƙasashen waje.

Cardoso ya ƙara da cewa CBN zai ci gaba da inganta yanayin gudanar da harkokin kuɗi ta hanyar bai wa sabbin masu gudanar da ayyukan hadahada lasisi, tallafa wa hanyoyin biyan kuɗi na dijital, da kuma haɗin gwiwa da bankuna, kamfanonin fintech da sauran masu ruwa da tsaki domin faɗaɗa shigar jama’a cikin harkokin kuɗi.

Ya jaddada cewa tilas ƙa’idoji su ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire tare da tabbatar da cewa duk cibiyoyin da ke kula da kuɗin jama’a, sarrafa biyan kuɗi ko adana bayanan kwastomomi suna gudanar da ayyukan su cikin gaskiya.

Daga ƙarshe, Cardoso ya ce CBN zai ci gaba da amfani da ƙa’idoji iri ɗaya ga dukkan cibiyoyin da ke fuskantar irin wannan haɗari, ba tare da la’akari da girman su, tsarin mallakar su ko fasahar da suke amfani da ita ba.

Sai dai ya ce cibiyoyin da ke da babban tasiri a kasuwa za a buƙaci su bi ƙa’idojin shugabanci da bin dokoki masu tsauri fiye da sauran.

Tags: Olayemi Cardoso
Previous Post

Rahoton CBN: An yi hadahadar kuɗi ta wayar hannu har adadin naira tiriliyan 372 cikin 2025

Next Post

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

Gwamnan Neja ya ba jami'ar AKUM motocin aiki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!