Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙarin albashi ga jami’an Rundunar Sojin Nijeriya da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da Gwamnatin Tarayya ta ce na inganta jin daɗin jami’an tsaro da ƙarfafa masu gwiwa wajen gudanar da ayyukan su.
Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Talata ta bayyana cewa kimanin jami’ai da sojoji 250,000 ne za su amfana da sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumba 2026.
A cewar sanarwar, jami’an da ke daga muƙamin Birgediya Janar zuwa Janar za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin ɗari, yayin da jami’an daga muƙamin Kanar zuwa Warrant Officer za su samu ƙarin kashi 50 cikin ɗari. Haka kuma, sojojin da ke daga muƙamin Parabiti (Private) zuwa Sitaf Saje za su amfana da ƙarin albashi mafi girma na kashi 80 cikin ɗari.
Sanarwar ta ƙara da cewa sabon tsarin zai ƙara yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa kan albashin jami’an sojin daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924 a duk shekara.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa na yaba wa jajircewa da sadaukarwar jami’an rundunar sojin wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan ƙasar nan.
Ya ce, “Mazan da matan da ke tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mu sun cancanci a tallafa masu tare da nuna musu godiya saboda hidimar da suke yi wa ƙasa. Gwamnatin mu za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin jami’an tsaro tare da samar musu da makamai da fasahohin zamani domin su gudanar da aikin su yadda ya kamata.”
Shugaban ya kuma jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun cigaba mai ɗorewa ba tare da ingantaccen tsaro ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen amfani da dukkan rundunonin tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
Tinubu ya yi kira ga jami’an rundunar sojojin da su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin wata alamar godiya daga gwamnati bisa irin hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa Nijeriya za ta yi nasara kan masu neman tada zaune tsaye da tarwatsa zaman lafiyar ƙasar.






