• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin rage kudin sufuri ta kan ba da lamunin sauya injinan mota zuwa na CNG

Wakilin Mu by Wakilin Mu
April 24, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin rage kudin sufuri ta kan ba da lamunin sauya injinan mota zuwa na CNG
Shugaban Shirin Shugaban Ƙasa kan Iskar Gas da motoci masu lantarki (Pi-CNG & EV), Barista Ismail Ahmed, tare da sauran manyan baƙi a wurin yarjejeniyar

Shugaban Shirin Shugaban Ƙasa kan Iskar Gas da motoci masu lantarki (Pi-CNG & EV), Barista Ismail Ahmed, tare da sauran manyan baƙi a wurin yarjejeniyar

Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin shirin nan na Shugaban Ƙasa kan Iskar Gas da motoci masu lantarki (Pi-CNG & EV), ta ƙulla wata yarjejeniya da manyan hukumomin kuɗi domin sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya hanyoyin samun bashi don sauya injinan motocin su daga masu amfani da fetur da dizil zuwa gas (CNG) da wutar lantarki.

Yarjejeniyar, wadda aka rattaba wa hannu a birnin Abuja, ta haɗa da shirin Pi-CNG & EV, da hukumar CrediCorp mai bayar da bashi ga masu sayayya, da kamfanin NCGC mai ba da tabbacin kuɗi, da kuma bankin Moniepoint.

Wannan shiri na Pi-CNG & EV yana ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin tsarin Renewed Hope, da nufin haɓaka amfani da makamashi mai tsafta, rage tsadar man fetur, da kuma rage gurɓatar yanayi a faɗin kasar nan.

Babban maƙasudin wannan haɗaka shi ne samar da tsari inda masu motocin ƙashin kan su, direbobin haya, da masu manyan motocin sufuri za su iya samun tallafin kuɗi cikin sauƙi domin biyan kuɗin sauya injinan motocin su ba tare da fuskantar matsin tattalin arziki ba.

A cewar jami’an gwamnati, wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gaba da tashi, inda aka kalli sauya injin zuwa na gas a matsayin hanya mafi sauƙi ga ‘yan kasa.

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban shirin, Barista Ismail Ahmed, ya bayyana cewa wannan yarjejeniya wani babban mataki ne na ganin an tabbatar da adalci da ɗorewa wajen sauya salon amfani da makamashi a ƙasar nan.

Ahmed ya fayyace cewa shirin ya ginu ne a kan abubuwa guda uku: Samuwa, Karɓuwa, da kuma Rahusa.

Ya bayyana cewa dole ne a samar da wuraren sauya injinan a ko’ina, a tabbatar wa jama’a cewa gas din ba shi da haɗari, sannan kuma a samar da hanyar biya cikin sauƙi.

“Ta hanyar wannan hadaka, talaka yanzu yana da damar samun bashin sauya injin motar sa ta hanyar bankunan da aka aminta da su, tare da tabbacin kuɗi daga gwamnati,” inji shi.

Ya ƙara da cewa wannan shiri ba wai kawai zai rage raɗaɗin tsadar sufuri ba ne, har ma zai samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasa a ɓangaren ƙera injina, gyaran motoci, da kuma sarrafa sassan motocin a cikin gida.

A nasu ɓangaren, shugabannin hukumomin da suka ƙulla yarjejeniyar, ciki har da Uzoma Nwagba na CrediCorp, Ezekiel Oseni na NCGC, da Tobi Amira na Moniepoint, sun jaddada aniyar su ta bayar da duk wani tallafi da ake bukata domin tabbatar da cewa wannan shiri ya kai ga nasara, domin rage raɗaɗin kudin sufuri da kuma kare muhalli.

Previous Post

Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma a matsayin Ministan Gidaje

Next Post

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar 'ya'yan maraina a asirce

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!