Hukumar bayar da lamuni ga ɗalibai ta ƙasa (NELFUND) ta fitar da kuɗi har naira (₦795,729,500) domin biyan kuɗin karatun ɗalibai 6,385 na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafiya (FULafia), Jihar Nasarawa.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙar godiya da jami’ar ta aika wa NELFUND mai ɗauke da sa hannun Shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammed Isa Kida.
A cikin wasiƙar, jami’ar ta nuna cewa an turo kuɗaɗen ne kashi uku tsakanin Fabrairu da Maris na bana kamar haka:
A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, ta biya wa ɗalibai 4,563 N565,249,500; sai ranar 24 ga Fabrairu, 2026 da aka biya wa ɗalibai 636 N82,189,000; sai kuma 3 ga Maris, 2026 da aka biya wa ɗalibai 1,186 N148,291,000.
Jimillar adadin ɗaliban ya kama 6,385 waɗanda aka biya masu N795,729,500.
Kida ya bayyana jin daɗin sa tare da yaba wa hukumar kan yadda take gudanar da ayyukan ta cikin gaskiya da riƙon amana.
Ya ce wannan tallafi babban abin farin ciki ne ga ɗaliban jami’ar, domin zai share masu hawaye tare da ba su damar ci gaba da karatun su ba tare da fargabar kuɗin makaranta ba.
Ya ce: “Tasirin da NELFUND take yi a rayuwar ɗaliban mu ba abin da za a iya kwatantawa ba ne. Mun gode ƙwarai da gaske kan sadaukarwar ku wajen bunƙasa ilimi a Nijeriya.”
Wannan tallafi yana zuwa ne a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope” na gwamnatin Tinubu da nufin tabbatar da cewa babu ɗalibin da ya rasa damar yin karatu saboda rashin hali.






