• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya za ta raba wa ‘manoman gaskiya’ tallafin dala miliyan 500 kai-tsaye

Wakilin Mu by Wakilin Mu
April 18, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya za ta raba wa ‘manoman gaskiya’ tallafin dala miliyan 500 kai-tsaye
Manoma a bakin aiki

Manoma a bakin aiki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta ta ganin cewa tallafin dala miliyan 500 da Bankin Duniya ya amince da shi, ya isa hannun manoma na haƙiƙa a faɗin ƙasar nan, maimakon karkata shi ga asusun banki na ‘yan siyasa.

Shugaban Hukumar ba da Tallafin Kuɗaɗen Haɗin Gwiwa na Ƙasa (NFC), Mista Emmanuel Atama, shi ne ya tabbatar da hakan cikin wata hira da aka yi da shi kwanan nan.

Atama ya ce an tsara shirin ne don ya amfani aƙalla manoma miliyan ɗaya, tare da magance matsalolin da suka dabaibaye shirye-shiryen da suka gabata.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka hana tallafin noma tasiri a baya shi ne tsoma bakin siyasa da kuma rashin sahihan bayanai.

Ya ce: “Yawancin shirye-shiryen da aka yi a baya sun fuskanci cikas sakamakon rashin isasshen bayani ga manoma da kuma tsoma bakin ‘yan siyasa, wanda hakan ya hana kuɗaɗen isa ga waɗanda aka yi niyya.”

Ya ƙara da cewa a wannan karon tsarin zai bambanta, musamman sakamakon haɗin gwiwa da Ministan Noma mai ƙwazo, wanda ya nuna shirye-shiryen cire duk wata sarƙaƙiya da ke kawo cikas wajen aiwatar da ayyukan hukumar.

Shugaban ya kuma bayyana cewa tattaunawar da suka yi da Bankin Duniya ta bankaɗo kurakuran da aka tafi da su a shirye-shirye irin su Anchor Borrowers Programme.

Saboda haka, wannan sabon tsarin zai mayar da hankali ne wajen gyara waɗannan kurakurai, inji shi.

A halin yanzu, hukumar ta riga ta fara zagaye domin wayar da kan manoma a jihohi daban-daban, inda ake ƙarfafa masu gwiwa su shiga ƙungiyoyin haɗin gwiwa.

Ya ce wannan shi ne zai ba da damar tantance su cikin sauƙi da kuma tabbatar da gaskiya wajen rabon tallafin.

Wani sabon salo da shirin zai zo da shi don toshe ƙofofin almundahana shi ne raba kayan aikin noma maimakon kuɗi tsantsa.

Atama ya fayyace cewa za a fi mayar da hankali wajen samar da takin zamani, iri, da injinan noma.

Ya ce idan har akwai buƙatar bayar da kuɗi kai-tsaye, ba zai wuce kashi 10% zuwa 15% na jimillar tallafin da manomi zai samu ba.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar ƙalubale hauhawar farashin abinci, inda ake fatan wannan tallafi zai bunƙasa samar da abinci a faɗin Nijeriya.

Tags: BankinDuniyaEmmanuel Atamamanomatallafi
Previous Post

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

Next Post

NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795

NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!