• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi

ALI KANO by ALI KANO
March 15, 2026
in Ilimi
A A
0
Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar da Ma’aikatar Ilimi domin ƙarfafa haɗin kai da kuma hanzarta aiwatar da gyare-gyare a ɓangaren ilimi na Jihar Kano.

Daraktan Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai a ranar Lahadi cewa, bayan wannan sake tsari, sabuwar ma’aikatar za ta ci gaba da aiki a matsayin Ma’aikatar Ilimi, inda za a ƙirƙiri wata sashen kula da Ilimi Mai Zurfi a cikin ta domin sa ido kan harkokin ilimin gaba da sakandare.

Ya ce wannan sashen zai kasance ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Dindindin, tare da samun goyon bayan ma’aikata da ake buƙata domin tabbatar da ingantaccen gudanar da cibiyoyin ilimi mai zurfi a jihar.

Ya ƙara da cewa: “A ƙarƙashin wannan sabon tsarin, dukkan hukumomi da ke ƙarƙashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi kamar Hukumar Ba da Tallafin Karatu za su koma Ma’aikatar Ilimi, yayin da jami’o’in mallakar jihar da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi za su kasance ƙarƙashin kulawar sabon sashen da aka kafa a cikin haɗaɗɗiyar ma’aikatar.”

Dawakin Tofa ya kuma ce: “Wannan mataki wani ɓangare ne na ci gaba da gyaran ɓangaren ilimi na jihar, wanda ke da nufin sake fasalta tsarin, kawar da maimaita ayyuka, inganta haɗin kai a manufofi a dukkan matakan ilimi, da kuma rage kuɗin gudanar da gwamnati.”

Ya ambato gwamnan yana cewa wannan gyara an tsara shi ne domin rage kuɗin gudanar da gwamnati tare da ƙara inganci, gaskiya da riƙon amana, da kuma inganta gaba ɗayan tsarin gudanar da ilimi a Jihar Kano.

Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa tana ci gaba da ƙudirin aiwatar da manyan gyare-gyare da za su farfaɗo da ɓangaren ilimi tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ga matasa.

A sakamakon haka, an umurci Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikata da su tabbatar da gaggauta da kuma daidaitaccen sake tsara ma’aikatun da abin ya shafa da sassan su.

Tags: Abba Kabir YusufKanoMa’aikatar Ilimi
Previous Post

Tinubu ya naɗa Fola Adeola shugaban kwamitin kawo sababbin matakan gyara a harkar fetur

Next Post

Garambawul da Tinubu yake yi yana ƙarfafa amincewar ƙasashen duniya ga Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja
Ilimi

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

August 29, 2026
Ilimi

Niger-SUBEB ta tabbatar da ƙarin girma ga malaman da suka cancanta

August 22, 2026
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris
Ilimi

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

August 20, 2026
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki
Ilimi

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

August 4, 2026
Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya
Ilimi

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

July 14, 2026
Next Post
Garambawul da Tinubu yake yi yana ƙarfafa amincewar ƙasashen duniya ga Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Garambawul da Tinubu yake yi yana ƙarfafa amincewar ƙasashen duniya ga Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!