Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa suna ƙara ƙarfafa amincewar ƙasashen duniya ga Nijeriya, tare da samar da sababbin damarmaki na kasuwanci da zuba jari.
Idris ya bayyana hakan ne a yau Litinin a birnin London, a lokacin wani taron manema labarai na duniya, gabanin ziyarar aiki da Shugaban Ƙasa Tinubu zai kai Birtaniya bisa gayyatar Sarki Charles na Uku.
Ya ce: “Wannan ziyara tana nuna tsohuwar dangantaka mai muhimmanci tsakanin Nijeriya da Birtaniya, wadda ta ginu kan ƙaƙƙarfar alaƙar diflomasiyya, tattalin arziki, al’adu da dimokiraɗiyya.”
A cewar sa, ziyarar za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannoni kamar kasuwanci da zuba jari, tsaro, magance sauyin yanayi, ilimi da fasahar zamani.
Idris ya ce gwamnatin Tinubu na aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki ne a ƙarƙashin shirin Sabunta Fata domin daidaita tattalin arziki, faɗaɗa damarmaki da bunƙasa cigaban ƙasa na dogon lokaci.
Ya bayyana manyan gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar, ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita tsarin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje.
A cewar sa: “Waɗannan gyare-gyare sun taimaka wajen dawo da gaskiya a harkokin kuɗin gwamnati, ƙarfafa ɗorewar tattalin arziki da inganta hasashen zuba jari.”
Ministan ya ƙara da cewa gyare-gyaren da aka yi a ɓangaren mai da iskar gas sun sa Nijeriya ta zama ƙasa mafi jan hankalin masu zuba jari a fannin makamashi a Afrika tsawon shekaru biyu a jere.
Ya ce: “An samu sama da dala biliyan 8 na sababbin zuba jari daga manyan kamfanonin duniya. Kowace dala daga cikin waɗannan zuba jari tana nufin samar da ayyukan yi ga ’yan Nijeriya, bunƙasa ƙwarewar fasaha, farfaɗo da al’ummomi da ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnatoci a matakai daban-daban.”
Idris ya bayyana cewa kwanan nan Nijeriya ta fita daga jerin ƙasashen da hukumar FATF ke sanya wa ido kan harkokin kuɗi, bayan aiwatar da gyare-gyare domin yaƙi da safarar kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da kuma haramtattun kuɗaɗen da ke gudana ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce wannan cigaba ya ƙara inganta sahihancin Nijeriya a tsarin kuɗaɗen duniya tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
Ministan ya kuma bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta Nijeriya ta haura dala biliyan 50 zuwa watan Fabrairun 2026, inda wani sashi na ajiyar aka adana a zinari a matsayin mataki na faɗaɗa hanyoyin ajiyar kuɗi.
Ya ce gwamnati na zuba jari sosai a manyan ayyukan ababen more rayuwa, ciki har da Babban Titin Gabar Teku na Legas zuwa Kalaba, Babbar Hanyar Sakkwato zuwa Badagiri da Bututun Iskar Gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK) domin inganta haɗin tattalin arziki da bunƙasa masana’antu.
Idris ya ƙara da cewa gyare-gyare a ɓangaren wutar lantarki da zuba jari a fannin ilimi, ciki har da asusun lamuni na ɗalibai, na nufin faɗaɗa samun wutar lantarki da damar ilimi mai zurfi.
Ya kuma ce gwamnati ta ƙarfafa musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro domin yaƙi da ta’addanci da ’yan bindiga, tare da faɗaɗa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, ciki har da Birtaniya da Amurka.
Daga ƙarshe, Ministan ya jaddada cewa: “Muna matuƙar darajta tsohuwar dangantakar da ke tsakanin mu da Birtaniya, kuma muna fatan ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a shekaru masu zuwa.”







