Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Cif Fola Adeola, ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa bankin Guaranty Trust Bank (GTB), a matsayin shigaban wani kwamiti na musamman wanda zai ɓullo da sababbin matakan gyare-gyare a ɓangaren harkar fetur.
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Adeola, wanda cikakken sunan sa Tajudeen Afolabi Adeolalisten, ɗan shekara 72, memba ne a Hukumar Afrika (Commission for Africa) kuma shugaban FATE Foundation.
Sauran membobin kwamitin su ne Ademola Adeyemi-Bero, Osagie Okunbor, Abubakar Suleiman, Adaeze Aguele, Farouk Gumel, Phillipa Osakwe-Okoye da Seyi Bella, yayin da Mofoluwasho Fadayomi ne sakatare.
A cewar Onanuga, an ɗora wa kwamitin alhakin tsara matakan gyare-gyare da za su bunƙasa harkar man fetur, su jawo ƙarin zuba jari, tare da ƙara wa tattalin arzikin ƙasar nan daraja.
Kwamitin zai riƙa kai rahoto kai-tsaye ga Shugaban Ƙasa duk wata, sannan zai gabatar da rahoton wucin-gadi bayan wata uku, yayin da ake sa ran kammala rahoton ƙarshe cikin wata shida.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da manyan tsare-tsare uku na gyara, ciki har da matakan sauya tsarin ɓangaren nan take.
A cewar sa, shirin zai bayar da damar samun jarin dala biliyan biyar zuwa 10, da kuma wani tsari na sauya tsarin makamashi na ƙasar nan na tsawon shekaru 10.







