Daraktan Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Ƙasar Amurka, Joe Kent, ya yi murabus daga muƙamin sa a yau Talata, yana mai bayyana damuwar sa kan hujjar kai hare-haren soja da Amurka ke yi a Iran, tare da cewa “ba zai iya da lamirin sa ba” ya goyi bayan yaƙin da gwamnatin Shugaba Trump take yi.
“Iran ba ta gabatar da wata barazana ta gaggawa ga ƙasar mu ba, kuma a bayyane yake mun fara wannan yaƙi ne saboda matsin lamba daga Isra’ila da kuma ƙarfin ƙungiyoyin tuntuɓar Amurka da ke goyon bayan ta,” inji Kent a wata sanarwa da ya wallafa a soshiyal midiya, yana yin zarge-zarge waɗanda Shugaba Donald Trump ya musanta.
Shi dai Kent, tsohon soja na rundunar Green Beret kuma ɗan takarar siyasa mai alaƙa da masu tsattsauran ra’ayi, an tabbatar da naɗin sa a watan Yulin bara da ƙuri’u 52-44. A matsayin shugaban cibiyar, shi ne yake jagorantar wata hukuma da ke da alhakin nazari da gano barazanar ta’addanci.
Murabus ɗin sa ya nuna cewa rashin jin daɗi game da yaƙin a cikin magoya bayan Trump ya kai har wani babban jami’i a gwamnatin jam’iyyar Republican zai aje aikin.
Wannan sauyin shugabanci a ɗaya daga cikin manyan hukumomin yaƙi da ta’addanci na ƙasar yana zuwa ne a lokacin da ake fuskantar ƙarin damuwa kan ta’addanci bayan hare-haren baya-bayan nan a wata majami’ar Yahudawa a Michigan da kuma wata jami’a a Virginia.

Hujjar kai wa Iran hari ce musabbabin murabus ɗin
Kent ya rubuta cewa dalilin murabus ɗin sa ya ta’allaƙa ne kan hujjar kai hare-hare kan Iran.
Trump ya bayar da dalilai mabambanta kan hare-haren, kuma ya ƙaryata zargin cewa Isra’ila ce ta tilasta Amurka ɗaukar mataki. Kakakin Majalisar Wakilai, Mike Johnson, ya nuna cewa Fadar White House ta yi imanin Isra’ila na da niyyar kai harin ita kaɗai, wanda ya sa shugaban Republican ya fuskanci “yanke shawara mai matuƙar wahala.”
Da yake magana da manema labarai a Ofishin Oval a ranar Talata, Trump ya ce tun da farko ya ɗauki Kent a matsayin “mai rauni a ɓangaren tsaro,” kuma idan wani a gwamnatin sa bai ɗauki Iran a matsayin barazana ba, to “ba ma buƙatar irin waɗannan mutane.”
“Ba mutane masu hankali ba ne, ko kuma ba su da basira,” inji Trump. “Iran babbar barazana ce.”
Shekara guda da ta gabata, yayin gabatar da sunan sa ga majalisa, Trump ya yaba wa Kent a matsayin mutum wanda ya “kwashe tsawon rayuwar sa yana farautar ‘yan ta’adda da masu aikata laifi.”
Mai magana da yawun Daraktan Leƙen Asiri na Ƙasa, Tulsi Gabbard, ba ta amsa tambayoyi nan take ba kan murabus ɗin Kent ko ra’ayin ta kan hare-haren.
‘Yan Democrat sun yi tsananin adawa da tabbatar da Kent saboda alaƙar sa da wasu masu tsattsauran ra’ayin siyasa da kuma ƙa’idojin makirci. Amma bayan murabus ɗin din sa, Sanata Mark Warner na Virginia, babban ɗan Democrat a Kwamitin Leƙen Asiri na Majalisar Dattawan Amurka, ya ce damuwar Kent kan yaƙin Iran ta dace.
“Na saba wa da dama daga cikin ra’ayoyin da ya daɗe yana yaɗawa, musamman waɗanda ka iya mayar da harkar leƙen asiri ta zama ta siyasa,” inji Warner. “Amma a wannan batu, yana da gaskiya: babu wata hujja mai ƙarfi da ke nuna barazana ta gaggawa daga Iran da za ta sa Amurka ta tsunduma cikin wani sabon yaƙi a Gabas ta Tsakiya.”
Sai dai Johnson ya ƙaryata iƙirarin Kent a taron manema labarai ranar Talata.
“Na samu dukkan bayanai. Dukkan mu mun fahimci cewa akwai barazana ta gaggawa, Iran na dab da mallakar ƙarfin nukiliya kuma suna ƙera makamai masu linzami da sauri fiye da yadda kowa a yankin zai iya bi,” inji Johnson.
Johnson ya ce ya gamsu cewa da Trump ya jira “da za a samu asarar rayuka masu yawa na Amurkawa, jami’an soja da sauran mutane, kuma wuraren mu za su lalace matuƙa.”
Tarihin soja na Kent da labarin rayuwar sa na sadaukarwa sun sa ya zama abin sha’awa ga magoya bayan Trump.
Kafin shiga gwamnatin Trump, Kent ya yi takara sau biyu ba tare da samun nasara ba don shiga Majalisa a jihar Washington. A matsayin soja na Green Beret, ya shiga yaƙi a aike-aike 11 kafin ya yi ritaya ya shiga ɗan CIA. Ya kuma fuskanci babban rashi: matar sa, ƙwararriyar masaniyar bayanan sirri ta rundunar ruwa (Navy), ta mutu a harin ƙunar baƙin wake a 2019 a Siriya, ta bar masa yara maza biyu ƙanana. Kent mai shekaru 45, tun daga lokacin ya sake aure.
A lokacin janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan a 2021 cikin ruɗani, Kent ya soki abin da ya kira yunƙurin gina ƙasa da ba daidai ba daga wasu a Washington, D.C.
“Wannan yana nuna girman kan mu,” inji Kent ga manema labarai yayin yaƙin neman zaɓe. “Rashin koyon darasi daga duk wannan yana nuna cewa akwai mutanen da ke cin gajiyar hakan suna gina sana’ar su a kan sa. Sun daɗe suna yin hakan a bayan wahala da gawar sojojin Amurka.”
A lokacin yaƙin neman zaɓen sa na 2022, Kent ya biya Graham Jorgensen, ɗan ƙungiyar soja ta masu tsattsauran ra’ayin siyasa Proud Boys, kudin ba da shawara. Haka kuma ya yi aiki tare da Joey Gibson, wanda ya kafa ƙungiyar Patriot Prayer, kuma ya samu goyon bayan wasu daga cikin masu tsattsauran ra’ayin siyasa.
A farkon yaƙin neman zaɓen sa, Kent ya amince cewa wani mai ba da shawara ya shirya kira don faɗaɗa tasirin sa a soshiyal midiya wanda Nick Fuentes, wani shahararren mai tasiri a siyasar tsattsauran ra’ayi, ya halarta—wanda ya taɓa cewa Yahudawa suna riƙe Amurka “a matsayin garkuwa” kuma ya taɓa yaba wa Hitler.
Daga baya Kent ya nesanta kan sa daga wannan alaƙa, yana mai cewa yana ƙin duk wani “wariya da nuna bambanci.”
A zaman tabbatar da naɗin sa a Majalisar Dattawa, Kent ya ƙi nesanta kan sa daga wata ƙa’idar makirci da ke cewa jami’an gwamnati ne suka haddasa harin 6 ga Janairu, 2021 a Capitol, da kuma iƙirarin ƙarya cewa Trump ya lashe zaɓen 2020 a kan ɗan Democrat Joe Biden.
‘Yan Republican sun yaba da ƙwarewar Kent a yaƙi da ta’addanci, suna nuna gogewar sa ta soja da ta leƙen asiri.
Sanata Tom Cotton, shugaban kwamitin leƙen asiri na jam’iyyar Republican, ya ce a jawabin sa Kent “ya sadaukar da rayuwar sa wajen yaƙi da ta’addanci da kuma kare lafiyar Amurkawa.”
(Tare da rahoton Associated Press)







