Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umurci kwamandoji a dukkan matakai da su kiyaye muhimman haƙƙin ɗan’adam da kuma tsaron dukkan ’yan Nijeriya yayin gudanar da ayyukan su na kundin tsarin mulki, yana mai jaddada cewa mutunta haƙƙin ɗan’adam yana da matuƙar muhimmanci ga nasarar ayyuka da kuma daidaiton ƙasa.
Muƙaddashiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Kanar Appolonia Anele, ta bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa COAS ya bayar da wannan umurnin ne a yau Talata, 17 ga Maris, 2026, yayin da yake gabatar da lacca kan falsafar jagorancin sa ga mahalarta Kwasa-kwasan Kwalejin Dabarun Yaƙi ta Nijeriya 10/2026 a Abuja.
Shaibu ya bayyana cewa falsafar jagorancin sa mai taken, “Inganta sauyin Sojojin Nijeriya zuwa rundunar da ta fi dacewa, shirin yaƙi, kuma mai juriya wadda za ta iya cika nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata cikin haɗin gwiwar hukumomi daban-daban,” ita ce ginshiƙin da ra’ayin sa na jagoranci ya ta’allaƙa kai.
Ya jaddada cewa bin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, ka’idojin gudanar da aiki (Rules of Engagement), da sauran tsare-tsare da aka kafa yayin gudanar da ayyuka, ba wai kawai yana kare fararen hula ba ne, har ma yana ƙara amincewar jama’a da kuma tallafa wa ayyukan da suka dogara da bayanan sirri.

COAS ya ce tsawon shekaru, sojojin Nijeriya sun ƙirƙiri dabaru daban-daban da suka tsara yadda suke tunkarar ƙalubalen tsaro da ke sauyi a ƙasar.
Ya kuma jaddada wa mahalarta su rungumi falsafar jagorancin sa, wadda ta ta’allaƙa kan manufar “Soja a Farko” (Soldier First Concept), wadda ke ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikata.
Ya bayyana cewa wannan manufa ta ginu ne kan muhimman ginshiƙai kamar ƙwarewa, ingantaccen gudanarwa, shirye-shiryen aiki, haɗin gwiwar dabaru, da jagoranci nagari, waɗanda ke da muhimmanci ga ingancin ayyuka.
Babban hafsan ya kuma shawarci mahalartan da su ba da muhimmanci ga haɓaka ƙwarewar waɗanda ke ƙarƙashin su ta hanyar horo mai tsari, inganci, kuma mai mayar da hankali kan manufa.
Ya jaddada cewa horo kan mutunta haƙƙin ɗan’adam da kare fararen hula yana da matuƙar muhimmanci, domin yana nuna ainihin ma’anar rantsuwar biyayya da dukkan jami’ai suke yi.

Kwamandan Kwalejin Dabarun Yaƙi ta Nijeriya, Manjo Janar Umar Alkali, ya gode wa COAS ɗin bisa ci gaba da goyon bayan sa ga kwalejin.
Ya ce laccar ta yi tasiri sosai ba ga mahalarta kaɗai ba, har ma ga cibiyar gaba ɗaya.







