• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Bukarti, Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 11, 2025
in Labarai
A A
0
Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Bukarti, Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa
Malam Nasir El-Rufai da Dakta Bulama Bukarti

Malam Nasir El-Rufai da Dakta Bulama Bukarti

Wani masanin tsaro, Dakta Bulama Bukarti, ya ƙaryata iƙirarin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Tarayya tana biyan kuɗaɗen fansa tare da samar da kayayyaki ga ’yan bindiga da ke addabar Nijeriya.

El-Rufai ya yi wannan zargi ne a shirin “Sunday Politics” na tashar talbijin ta Channels, inda ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tsaro a kan gwamnati.

Sai dai a martanin sa, Bukarti ya ce kalaman El-Rufai ba su da tushe, yana mai bayyana su da cewa “siyasa ce tsagwaron ta, babu gaskiya.”

Ya bayyana cewa babu wata doka ko manufa da ta bai wa gwamnati damar biyan ’yan bindiga ko kuma tallafa musu.

A cewar sa, kuɗaɗen fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan waɗanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa.

Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.

Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.”

Ya yi gargaɗin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin waɗannan maganganu an taɓa yi a kan gwamnatocin baya ma.

Yayin da yake bayani kan tsarin rundunar sojoji, Bukarti ya jaddada cewa shugaban ƙasa ne kaɗai yake da ikon bayar da umarnin ɗaukar matakin soja.

Ya ce gwamnoni, ministocin tsaro da ma mai ba da shawara kan harkokin tsaro ba su da wannan iko.

A cewar sa, tsarin umurni daga shugaban kasa yake farawa zuwa Babban Hafsan Soja, sannan daga can zuwa kwamandojin filin daga.

A ƙarshe, Bukarti ya ce magance matsalolin tsaro a Nijeriya na buƙatar dogon lokaci, hadin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da ’yan kasa, tare da tsaurara matakan yaƙi da cin hanci da rashawa.

Previous Post

Tinubu Ya Umurci Majalisar Zartarwa ta Ƙasa Da Ta Gaggauta Ɗaukar Matakin Rage Farashin Abinci 

Next Post

Tsohon Shugaban NNPCL, Kyari ya Kwana Hannun EFCC Yana Amsa Tambayoyi

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Tsohon Shugaban NNPCL, Kyari ya Kwana Hannun EFCC Yana Amsa Tambayoyi

Tsohon Shugaban NNPCL, Kyari ya Kwana Hannun EFCC Yana Amsa Tambayoyi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!