Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da ta gaggauta ɗaukar matakan da za su saukar da farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan.
Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba, inda ya ce Shugaba Tinubu ya bayar da umurnin tabbatar da cewa ana samun sauƙin jigilar amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni ba tare da tsadar sufuri ba.
A cewar sa, shugaban ƙasar yana son a samar da tsarin da zai tabbatar da samun abinci mai araha, mai inganci, kuma mai wadatar gina jiki ga ’yan Nijeriya, ba kawai samun wadataccen abinci ba.
Ministan ya ce gwamnati za ta ƙaddamar da shirin ‘Farmer Soil Health Scheme’ don inganta amfanin gona, da kuma sabunta tsarin haɗin kan manoma domin samar da kuɗeɗe da ƙarfafa gwiwar manoma a karkara.
Ya ƙara da cewa Tinubu yana da babban buri a fannin haɗin kan manoma a matsayin wata hanya ta bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.
Tun a watan Yuni, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa Nijeriya tana kan hanya wajen cimma burin ’yancin samar da abinci a ƙasar, inda ya jaddada buƙatar kasar ta dogara da kan ta wajen samar da abincin da za ta ci.







