Hukumar EFCC ta tsare tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari bayan ya amsa gayyatar da ta yi masa a ranar Laraba.
Kyari ya kai kan sa hedikwatar EFCC da masanin ƙarfe 2:30 na rana, inda ba a yi wata-wata ba, aka ci gaba da tsare shi, bayan ya amsa tambayoyi da suka danganci zargin salwantar maƙudan kuɗaɗe a kamfanin man fetur na NNPCL.
Daga cikin zarge-zargen da ake masa, akwai binciken yadda aka kashe Dala biliyan 7.2 wajen gyaran matatun man Najeriya guda huɗu, amma suka kasa tace galan ɗaya.
Kafin tsarewar da aka yi masa, a watannin baya an gayyace shi hukumar, lamarin da ya kai har EFCC ta kulle tare da riƙe waɗansu asusun banki na Kyari ɗin, waɗanda majiyoyi suka ce cike maƙil suke da kuɗaɗe.
Tuni dai EFCC ta tabbatar da cewa lallai Kyari ya na hannun ta, amma ba ta yi ƙarin haske ba. Ta dai ce ana ci gaba da binciken sa.
Tsawon shekaru da dama Najeriya na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen aikin gyaran matatun man fetur huɗu da take da su a Warri, Fatakwal, Legas da Kaduna, amma haƙa ba ta cimma ruwa ba, aka wayi gari attajiri Aliko Ɗangote ya gina ƙasaitacciyar matatar fetur Legas.







