• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta fara yajin aiki na mako biyu

ALI KANO by ALI KANO
October 12, 2025
in Ilimi
A A
0
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta zaɓi Farfesa Piwuna a matsayin Shugaba
Farfesa Chris Piwuna, Shugaban ASUU

Farfesa Chris Piwuna, Shugaban ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bayyana cewa za ta fara yajin aiki na mako biyu daga gobe Litinin saboda kasa cika alƙawarin da gwamnati ta yi mata.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau a Abuja.

Piwuna ya ce an yanke shawarar hakan ne bayan gazawar da Gwamnatin Tarayya ta yi na biya wa ƙungiyar buƙatun ta bayan ƙarewar wa’adin kwana 14 da ta gindaya.

A cewar sa, manufar wa’adin da ƙungiyar ta bayar a ranar 28 ga Satumba ita ce a ba gwamnati lokaci ta warware matsalolin da suka daɗe ana tataɓurza a kan su duk da zaman tattaunawa da aka sha yi.

Ya ce: “Waɗannan matsalolin sun haɗa da kammala yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da ASUU ta 2009 da biyan albashin watanni uku da rabi da gwamnati ta riƙe.

“Sauran su ne farfaɗo da tare da ci gaba da ɗaukar nauyin jami’o’in gwamnati, biyan sauran kashi 25 cikin ɗari na bashin albashi da aka biyo, da kuma bashin ƙarin girma na tsawon shekaru huɗu.”

Ya ƙara da cewa a kuma biya kuɗin da aka zabtare na wasu ayyukan musamman da malamai suka yi sannan a daina musguna wa malaman jami’o’in Legas (LASU), KSU, da FUTO a matsayin matsalolin da ba a warware ba.

Piwuna ya bayyana matsayin da gwamnati ta ɗauka kan waɗannan al’amurra da cewa jan faɗa ne da tsokana kurum.

Ya ce: “Takardun da wakilan gwamnati suka kawo wajen zaman tattaunawa sun yi hannun riga da shawarwarin da kwamitin da Alhaji Yayale Ahmed ya jagoranta ya gabatar a baya.”

Saboda haka ya yi kira ga ɗalibai da iyaye da dukkan ‘yan Nijeriya da su fahimci halin da ake ciki, yana mai cewa an ɗauki wannan mataki ne domin a tilasta wa gwamnati ta inganta tare da sauya fasalin tsarin ilimi na ƙasar nan.

Ya ce: “Da wannan muke bada umurni ga dukkan rassan ƙungiyar ASUU da su janye daga ayyukan su daga sha-biyun Daren Litinin, 13 ga Oktoba.

“Wannan yajin aiki na gargaɗi za a yi shi gama-gari kuma cikakke.”

Tags: ASUUFarfesa Chris Piwunamalaman jami'o'iyajin aiki
Previous Post

Dalilan da suka haifar da jan-ƙafa wajen aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 – Yakubu

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Ɗanlami Nmodu murnar zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Onlayin

Related Posts

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja
Ilimi

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

August 29, 2026
Ilimi

Niger-SUBEB ta tabbatar da ƙarin girma ga malaman da suka cancanta

August 22, 2026
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris
Ilimi

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

August 20, 2026
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki
Ilimi

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

August 4, 2026
Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya
Ilimi

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

July 14, 2026
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Ɗanlami Nmodu murnar zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Onlayin

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Ɗanlami Nmodu murnar zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Onlayin

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!