• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Dalilan da suka haifar da jan-ƙafa wajen aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 – Yakubu

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 11, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Dalilan da suka haifar da jan-ƙafa wajen aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 – Yakubu
Dakta Tanimu Yakubu

Dakta Tanimu Yakubu

Babban Darakta a Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya, Dakta Tanimu Yakubu, ya bayyana wa Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Darattawa dalilan da suka haifar da samun Jan-ƙafa wajen kammala aiwatar da ayyukan kasafin kuɗaɗe na shekarar 2024 da na 2025.

Da yake jawabi a gaban kwamitin a ranar Alhamis, a Majalisar Dattawa, Abuja, Yakubu ya ce ƙoƙarin aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 ya haɗu da tangarɗa, inda ƙwararren masanin tattalin arzikin ya ci gaba da cewa an samu naƙasu da ƙarancin kuɗaɗen shigar da aka yi hasashen samu a lokacin da ake tsara kasafin kuɗaɗe.

“Shekarar ta kasance mana da tsauri sosai, ta yadda yawancin hasashen geji da mizanin awon da muka yi wa kasafin 2024 da na 2025, ya zo ƙasa sosai da yadda muka zata,” inji shi.

Ya ƙara da cewa mizanin awon farashin ɗanyen mai da suka tsara kasafin da shi na Dala 75 ($75) kowace ganga, bai ɗore ba.

Ya ce farashin gangar ɗanyen mai ya riƙa sauka da $10 har da $15 ƙasa da mizanin awon kasafin kuɗaɗe.

Yakubu ya alaƙanta wannan giluniya da farashin ya riƙa yi cewa matsala ce da ta shafi duniya, ba Najeriya kaɗai ba.

Babban Daraktan ya ƙara bayar da dalilin tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyaki suka haifar da cikas. Sannan ya haddasa ƙarin yawan basussukan kuɗaɗen da Najeriya ke biya, wanda hakan ya riƙa haifar da rashin yawan kuɗaɗen da za a aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da su.

Yakubu ya ci gaba da cewa sababbin dokokin da ke shimfiɗe cikin Dokar Man Fetur ta PIA ta 2022, sun rage yawan kuɗaɗen shigar da Gwamnatin Tarayya ke samu.

Ya ce, “A ƙarƙashin Dokar Fetur ta PIA, ana bada kashi 30 na kuɗaɗen shiga na fetur akan ladar gudanar da harkokin dillancin man Najeriya ga NNPC Limited.

“Sai kuma wani 30 na ribar ɗanyen mai da gas shi ma yana tafiya wajen aikin haƙar mai da iskar gas a wasu wurare da ba su da tabbas, ko haƙar ma’adanan na da wasu matsaloli da ya buwayi yin haka. Yayin da kuma Gwamnatin Tarayya ke ɗauke da nauyin tafiyar da ayyukan NNPC.

“Saboda haka wannan ya haddasa datse yawan kason kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke samu da kusan kashi 70.”

Ya ƙara bayar da dalilin yadda adadin yawan ɗanyen mai da aka riƙa haƙowa ya gaza kai adadin yawan wanda aka yi hasashen samu. Wannan a cewar babban daraktan ya takure kuɗaɗen shiga tare da kawo tsaiko wajen biyan kuɗaɗen manyan ayyuka.

A taron dai Ministan Harkokin Kuɗaɗe, kuma Ministan Lura da Tattalin Arziki, Wale Edun da Akanta-Janar na Tarayya, Shamsuddeen Ogunjimi, duk sun yi jawabai dangane da batun kasafin.

A nasa jawabin bayan taron, Shugaban Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Darattawa, Sanata Mohammed Sani Musa, ya bayyana wa manema labarai dakatar da gabatar wa Majalisa sabon kasafi har sai an fara gabatar wa majalisar da cikakkun bayanan kasafin 2024 da na 2025 a ranar 23 ga Satumba, 2025 tukunna.

Tags: Kasafin KuɗiTanimu Yakubu
Previous Post

Tinubu ya rattaba hannu a dokar kafa cibiyoyin horas da ‘yan sanda

Next Post

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta fara yajin aiki na mako biyu

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta zaɓi Farfesa Piwuna a matsayin Shugaba

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta fara yajin aiki na mako biyu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!