• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Wasanni

WAFU 2025: Gwamnatin Tarayya Ta Yabi Super Falcons a Matsayin Zakarun Afrika

WAKILIN MU by WAKILIN MU
July 28, 2025
in Wasanni
A A
0

 

GWAMNATIN Tarayya a yau ta shirya kyakkyawar tarba ga ‘yan ƙwallon mata, wato Super Falcons, bayan dawowar su daga Rabat, babban birnin ƙasar Morokko, inda suka lashe gasar Kofin Afrika na Mata ta CAF ta shekarar 2024 a matsayin zakarun Afrika.

A cikin wata sanarwa, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana nasarar a matsayin fiye da cin gasar wasanni kawai, yana mai cewa, “nasarar wata shaida ce ta jajircewa, ƙwazo, da ƙarfin gwiwar ‘yan Nijeriya wadda Super Falcons ta nuna.”

Da yake jawabi a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnatin Tarayya, Ministan ya yaba wa ‘yan wasa, da masu horaswa da tawagar ma’aikatan su bisa jajircewar su da sadaukarwar su.

Ya ce: “Kun zamo abin koyi ga matasa a Nijeriya, kuma kun nuna irin tasirin da wasanni suke da shi wajen haɗa kan jama’a da kuma ƙarfafa gwiwa.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu tana da cikakken ƙudiri wajen ci gaba da saka jari a fannin wasanni da tallafa wa ‘yan wasa, ta hanyar samar da ababen more rayuwa da matakan da za su ba su damar yin fice.

Yayin da Super Falcons ke shigowa Abuja, ministan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su fito su tarbi ƙungiyar a lokacin tafiyar da za su yi daga ƙofar birnin Abuja zuwa Dandalin Eagle har zuwa Fadar Shugaban Ƙasa, inda za a karɓe su a hukumance.

“Super Falcons sun ɗaga tutar Nijeriya sama, sun kuma kawo farin ciki ga miliyoyin ‘yan ƙasa. Barkan ku da dawowa, zakarun Afrika!” inji shi.

A ranar Asabar dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Super Falcons ɗin murna kan nasarar da suka samu a gasar.

A takardar sanarwa wadda Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai, Mista Bayo Onanuga, ya rattaba wa hannu, Tinubu ya ce, “Gagarumar nasarar da Super Falcons suka samu a daren yau a Rabat, inda suka zo daga ‘yan sahun baya suka buge Marokko da ke da ƙarfi kuma a gaban ‘yan kallo masu shauƙi, alama ce ta jan halin da ‘yan Nijeriya suke da shi.

“Tare da aiki tuƙuru, sadaukarwa da jajircewar, kun cimma nasarar da ƙasar nan take fatan samu kuma take addu’a a kai. Ƙasar nan tana sa ran yin kyakkyawar tarba ga gwarzayen mu. Muna murna! Nijeriya tana ɗokin ku.”

Previous Post

Yilwatda Ya Maye Gurbin Ganduje A Matsayin Sabon Shugaban APC

Next Post

Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Super Falcons Da Kyautar Dala 100,000 Da Kuma Gida Kowannen Su

Related Posts

Ku jaruman gaske ne na ƙasar mu, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta faɗa wa ‘yan wasa a taron kammala Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na 3
Wasanni

Ku jaruman gaske ne na ƙasar mu, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta faɗa wa ‘yan wasa a taron kammala Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na 3

April 3, 2026
CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko
Wasanni

CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko

March 17, 2026
Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON
Wasanni

Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON

January 17, 2026
AFCON: Gwamnatin Tarayya ta zaburar da Super Eagles gabanin wasan kusa da na ƙarshe da Marokko
Wasanni

AFCON: Gwamnatin Tarayya ta zaburar da Super Eagles gabanin wasan kusa da na ƙarshe da Marokko

January 14, 2026
AFCON 2025: Lookman ya zaburar da Eagles zuwa nasarar 3-2 kan Tunisiya, sun samu tikitin zuwa zagaye na gaba
Wasanni

AFCON 2025: Lookman ya zaburar da Eagles zuwa nasarar 3-2 kan Tunisiya, sun samu tikitin zuwa zagaye na gaba

December 28, 2025
Bankwana da 2025: Shekarar da Harry Kane ya ci ƙwallaye 60 a Bayern, Mbappe ya ci 59 a Madrid
Wasanni

Bankwana da 2025: Shekarar da Harry Kane ya ci ƙwallaye 60 a Bayern, Mbappe ya ci 59 a Madrid

December 23, 2025
Next Post

Tinubu Ya Gwangwaje 'Yan Super Falcons Da Kyautar Dala 100,000 Da Kuma Gida Kowannen Su

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!