Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) ta ƙwace kofin gasar cin kofin nahiyar ƙasashen Afrika (AFCON) na 2025 daga hannun Senegal da suka lashe gasar a watan Janairu, tare da ayyana Morokko a matsayin zakarun gasar.
An ce wasu ‘yan wasan Senegal sun bar filin wasa na ɗan lokaci a ƙarshen wasan domin nuna rashin amincewa da wani hukunci da alƙalin wasa ya yanke.
CAF ta bayyana a cikin wata sanarwa yau Talata cewa “an ɗauki ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal a matsayin wadda ta yi watsi da wasan,” duk da nasarar da suka samu da ci 1-0 a wasan ƙarshe, inda aka mayar da sakamakon a hukumance zuwa 3-0 aka ba Morokko nasara.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Morokko (FRMF) ta ce a cikin wata sanarwa: “Matakin da ta ɗauka ba domin ƙalubalantar yadda ƙungiyoyi suka taka leda ba ne, sai dai domin neman a bi dokokin gasar yadda ya kamata.”
Mintuna kaɗan kafin ƙarshen wasan, wasu magoya bayan Senegal sun yi yunƙurin kutsawa cikin fili, yayin da ‘yan wasan Senegal suka dakatar da wasan na kusan mintuna 20 domin nuna rashin amincewa da bugun fanareti da aka bai wa Morokko a ƙarshen wasan.
An bayar da bugun fanaretin ne a ƙarshen lokacin wasa ba tare da an zura ƙwallo ba, lamarin da ya jawo ficewar ‘yan wasan Senegal daga fili na wani lokaci, wanda ya haddasa tsaiko na mintuna 20.
Bayan Senegal ta dawo wasa, Brahim Diaz ya kasa cin fanaretin, sannan Pape Gueye ya ci ƙwallon da ta ba Senegal nasara a ƙarin lokaci.
A wasan ƙarshe na AFCON na watan Janairu, Senegal ta bai wa Morokko mamaki inda ƙwallon da Pape Gueye ya ci ta ba su nasarar 1-0 a ƙarin lokaci, a wasan da ya kasance cike da rikici sakamakon ce-ce-ku-ce kan bugun fanareti.
Brahim Diaz ya kusa bai wa Morokko kofin lokacin da ya zo ya buga fanareti a minti na 24 na ƙarin lokaci a ƙarshen wasan.
Sai dai mai tsaron ragar Senegal, Edouard Mendy, ya daƙile ƙwallon cikin sauƙi, bayan ɗan wasan na Real Madrid ya buga ƙwallo mai rauni, wanda aka ce tsaikon kusan mintuna 20 bayan bayar da fanaretin ya dagula masa hankali.
Alƙalin wasa daga Kongo, Jean-Jacques Ndala, shi ne ya bayar da fanaretin a ƙarshen ƙarin mintuna takwas bayan duba na’urar VAR kan wata taƙaddama da aka yi wa Diaz a cikin akwatin bugun fanareti daga ɗan wasan baya na Senegal, El Hadji Malick Diouf.
Diaz da sauran ‘yan wasan Morokko tare da masu horar da su sun yi kakkausar suka ga alƙalin wasa ya sake duba hotunan, amma sai hukuncin bayar da fanaretin ya fusata Senegal da magoya bayan su.
Yayin da yawancin ‘yan wasan Senegal suka fice daga fili, wasu daga cikin magoya bayan su sun jefa kujeru da wasu kayayyaki, tare da ƙoƙarin shiga cikin filin wasan.
Daga bisani jami’an tsaro da masu kula da wasa suka daƙile su, inda daga baya farin cikin su ya sauya zuwa mamaki da farin ciki bayan an hana fanaretin shiga raga.
Tun da farko, ‘yan wasan Senegal sun fusata da hukuncin alƙalin na soke wata ƙwallo da suka ci a minti na biyu na ƙarin lokaci, bayan Abdoulaye Seck ya buga ƙwallo da kai daga bugun kusurwa ta bugi sanda, sannan Ismaila Sarr ya ci ƙwallon da ta dawo.
Bayan Diaz ya kasa cin fanareti, alamu sun nuna cewa Senegal za ta ci ƙwallo, kuma hakan ya faru a minti na huɗu na ƙarin lokaci, wanda ya girgiza magoya bayan gida a cikin taron mutane 66,526 da ke dandalin wasa na Prince Moulay Abdellah.







