Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yaba wa ‘yan wasan da suka halarci Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na uku, inda ta bayyana su a matsayin “jaruman gaske na ƙasar mu.”
Sanata Tinubu, wadda ta yi jawabi a wajen rufe gasar da aka gudanar a Dandalin Wasannin Ƙasa na Moshood Abiola da ke Abuja a yau, ta yaba da juriyar ‘yan wasan a tsawon gasar, tana mai cewa: “Na yaba wa ‘yan wasan da suka fito daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.
“Kun nuna jarumtaka, juriya da ƙima. Kun nuna mana cewa ƙarfin ruhin ɗan’adam ba shi da iyaka.
“A matsayi na na uwa, na ji ƙwarin gwiwa matuƙa. Ba wai a ‘yan wasa kawai nake kallon ku ba, sai dai ‘ya’ya maza da mata na Nijeriya masu ƙudiri, waɗanda suka zaɓi jarumtaka maimakon tsoro, nagarta maimakon uzuri da iyakancewa. Ku ne jaruman gaske na ƙasar mu.”
Uwargidan Shugaban Ƙasar, wadda matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, ta wakilta, ta ƙara da cewa: “A matsayin mu na ƙasa dole ne mu ci gaba da gina al’umma mai haɗa kowa da kowa, inda dukkan naƙasassu za su samu tallafi, girmamawa da ƙarfafa gwiwa, ba a fannin wasanni kaɗai ba har ma a fagagen ilimi, kiwon lafiya, aiki da shugabanci.
“Wannan hangen nesa ya yi daidai da ajandar Sabuwar Fata ta Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, wanda gwamnatin sa take da ƙudirin tabbatar da cewa babu wanda za a bari a baya, kamar yadda aka nuna ta hanyar naɗa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin naƙasassu.”
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma yaba da sauye-sauyen da ake yi a harkar wasanni ƙarƙashin Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), Malam Shehu Dikko.
Ta ce: “Na yaba wa Shugaban NSC, Malam Shehu Dikko, da abokan aikin sa kan nasarar shirya wannan gasa da kuma ƙoƙarin su na sake fasalin wasannin Nijeriya.”

Da yake jawabi a taron, Malam Dikko ya yaba wa ‘yan wasan naƙasassu na Nijeriya bisa yadda suke ɗaga darajar ƙasar a taswirar wasannin duniya.
Ya ce: “‘Yan wasan mu naƙasassu sun cancanci dama. Sun cancanci horo mai kyau. Sun cancanci ingantattun kayan aiki. Sun cancanci hanyoyi tsararru na cigaba. Kuma sun cancanci tsarin da zai gane baiwar su, ya tallafa wa burin su, ya ba su damar bunƙasa.
“Wannan yana da matuƙar muhimmanci domin sau da dama ‘yan wasan mu naƙasassu sun nuna kishin ƙasa.
“Sun ci gaba da kawo gagarumar nasara, suna lashe lambobin yabo ga ƙasar mu, suna kuma ɗaga martabar Nijeriya a idon duniya.
“A fannoni da dama, sun kasance jakadun mu mafi amincewa a duniya, suna fafatawa da jarumtaka, suna mamaye wasanni da nagarta, kuma suna kawo ɗaukaka ga ƙasa.”
Dikko ya ƙara da cewa ya kamata a ba ‘yan wasa naƙasassu cikakkar kulawa da girmamawa saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen ɗaga sunan Nijeriya.
“Abu mafi ƙaranci da ya kamata mu yi masu shi ne samar da tsarin da zai dace da ƙoƙarin su ta hanyar tallafi, zuba jari da girmamawa. Wannan shi ne alƙawarin Hukumar Wasanni ta Ƙasa.

“Za mu ci gaba da aiki da duk masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa bunƙasar ‘yan wasa, inganta walwalar su, faɗaɗa damar su, da tabbatar da cewa wasannin naƙasassu sun samu kulawa da zuba jarin da suka dace.”
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗa kowa da kowa, domin cika ƙudirin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na bunƙasa wasanni a kowane mataki.
Ya ce: “Saƙon wannan gasa a bayyane yake: kowane ɗan Nijeriya yana da muhimmanci, kowace baiwa tana da muhimmanci, kuma babu wanda za a bari a baya.
“A Hukumar Wasanni ta Ƙasa, wannan ita ce alƙiblar da muke bi. A ƙarƙashin ajandar Sabuwar Fata da Wadata ga Kowa ta Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, muna sake fasali da sake gina ɓangaren wasanni domin ya zama mai haɗa kowa, mai inganci, mai tsare gaskiya, kuma mai tasiri.
“Abu mafi muhimmanci shi ne wannan gyara yana gudana ne da cikakken goyon baya da amincewar Shugaban Ƙasa, wanda ya ɗauki matakai masu muhimmanci domin mayar da wasanni ginshiƙi na tattalin arziki da ƙasa.”
Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa, ya jaddada muhimmancin wasanni wajen gyaran al’umma.
Ya ce: “‘Yan wasan sun tuna mana cewa ainihin ƙarfi yana fitowa ne daga zuciya da tunani. Sun nuna cewa ƙalubale ba sa ƙayyade iyawar mu.
“Wannan gasa ta nuna manufar wadata ga kowa ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Babu wanda ya kamata a bari a baya. Dole ne mu yaba wa NSC kan wannan haɗa kai a wasanni.”

A nata jawabin, Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin kan ƙasa ta hanyar wasanni, tare da nuna alaƙar da ke tsakanin ilimi da wasanni wajen bunƙasar ƙasa.
Ta ce: “Ilimi da wasanni suna da buri ɗaya wajen ƙarfafa bunƙasar ƙasa da haɗin kai.
“Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tana ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke ƙarfafa haɗa kai da kuma haɗin kan ƙasa—abin da wannan Gasar Naƙasassu take wakilta kenan.”
A jawabin buɗe taron, Darakta Janar na NSC, Hon. Bukola Olopade, ya yaba wa ‘yan wasa naƙasassu kan yadda suka ɗaga matakin gasar Abuja 2026.
Ta bakin wakilin sa, Lekan Abari, ya ce: “Matakin wannan gasa ya yi matuƙar ƙarfi. Ba mu yi mamaki ba, domin ‘yan wasan mu naƙasassu sun riga sun yi fice a duniya.
“Su ne ‘yan wasan da ke kafa tarihi a manyan gasanni na duniya, don haka ba mu sa ran ƙasa da haka ba. Sun ba mu fata cewa za su fi haka a gaba.”
Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta NSC, Dr. (Mrs) Kehinde Ajayi, ta bayyana a cikin sanarwar manema labarai cewa babban abin jan hankali a taron shi ne bai wa Jihar Enugu kofin zakara na Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na 3 da Uwargidan Shugaban Ƙasa ta yi.
Jihar Inugu ce ta zo ta ɗaya da lambobin yabo 40 na zinariya, 8 na azurfa da 7 na tagulla; Jihar Bayelsa ta zo ta biyu da zinariya 25, azurfa 30 da tagulla 34; Ido ta zo ta uku da zinariya 25, azurfa 14 da tagulla 12; Ribas ta zo ta huɗu da zinariya 21, azurfa 21 da tagulla 17; yayin da Legas ta zo ta biyar da zinariya 20, azurfa 23 da tagulla 20.







