A ranar Asabar ne Nijeriya ta tabbatar da tsallakewa zuwa zagayen fitar da kai-tsaye na Gasar Kofin Nahiyar Afrika ta 2025 (AFCON), bayan samun nasara mai ƙayatarwa da ci 3-2 a rukunin C kan Tunisiya a filin wasa na Complexe Sportif de Fes da ke Morocco.
Victor Osimhen ne ya buɗe ƙwallo a ƙarshen rabin farko, inda ya kai ƙwallon kai cikin raga bayan Ademola Lookman ya aiko masa da ita, bayan Super Eagles sun yi asarar dama tun da fari.
Kyaftin Wilfred Ndidi ya ƙara wa Nijeriya ci na biyu minti biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, inda ya kai ƙwallo kai daga bugun ƙusurwa mai lanƙwasa da Lookman ya turo, ya kuma ci ƙwallon sa ta farko a matakin ƙasa da ƙasa.
Daga bisani Lookman ya kammala gagarumin wasan sa da ci na uku a minti na 67, inda ya zura ƙwallo cikin natsuwa bayan Osimhen ya ba shi taimako ba tare da son kai ba, lamarin da ya sa Super Eagles suka mamaye wasan gaba ɗaya.
Tunisiya ta rage tazarar a minti na 74 ta hannun bugun kai na Montassar Talbi, kafin Ali Abdi ya ci bugun daga-kai-sai-gola a ƙarshen wasan, wanda ya sa wasan ya ɗauki zafi.
Sai dai Super Eagles sun tsaya daram har zuwa ƙarshen wasan, suka samu nasarar su ta biyu a jere a gasar, tare da tabbatar da matsayin su a zagaye na 16 na AFCON 2025.

Ƙwallon da Osimhen ya ci ita ce ta 32 a wasanni 46 da ya buga wa Nijeriya, inda ya rage masa ƙwallaye biyar kacal ya kai tarihin marigayi Rashidi Yekini a tarihin ƙwallon ƙasa.
Kyakkyawar rawar da Ndidi ya taka a tsakiya da kuma ƙwallon da ya ci sun ƙara nuna ƙarfafa ikon Nijeriya, yayin da Eagles suka sake yin murnar nasara mai ƙara ƙwarin gwiwa a Morokko.
Yanzu Nijeriya ce ke kan gaba a rukunin C na AFCON da maki shida, bayan samun nasara biyu daga wasanni biyu da ta buga.
Tunisiya na da maki uku a matsayi na biyu, yayin da Cranes na Uganda da Taifa Stars na Tanzaniya, waɗanda suka tashi canjaras 1-1 a ɗayan wasan rukunin C, suke a matsayi na uku da na huɗu da maki ɗaya-ɗaya.
A rukunin D kuma, Jamhuriyar Benin ta doke Botswana da ci 1-0 don ci gaba da fatan kaiwa zagaye na 16, yayin da Senegal ta tashi kunnen doki 1-1 da DR Kwango a wasa mai matuƙar zafi.
Da yake magana bayan wasan, Frank Onyeka ya bayyana rashin jin daɗin sa kan ƙwallaye biyu da Eagles suka bari aka ci su, yana mai cewa ƙungiyar za ta iya yin fiye da haka.
“Na ji takaici yadda Tunisiya ta ci mana ƙwallaye biyu, musamman bugun daga kai sai mai tsaron gida da kuma bugun tsaye. Ina ganin mun yi wasa mai kyau, mun yi ƙoƙarin bin umarni,” inji shi.
Ya ce ƙungiyar za ta tunkari wasan ƙarshe na rukuni da Uganda kamar yadda suka buga da Tunisiya.
Haɗuwar Super Eagles da Tunisiya a matakin rukuni na AFCON 2025 ta zama karo na bakwai da suka haɗu a gasar.
Eagles sun doke su sau uku, yayin da Tunisiya ta yi nasara sau ɗaya. Sauran haɗuwar su biyu sun ƙare ne da bugun fenariti, inda kowanne ɓangare ya yi nasara sau ɗaya.
Super Eagles za su kara da Uganda a wasan su na ƙarshe na rukuni a ranar Talata da ƙarfe 4:00 na yamma a Fes, yayin da Tunisiya za su koma Rabat domin fafatawa da Tanzaniya a lokaci guda.







