• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, October 2, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Yilwatda Ya Maye Gurbin Ganduje A Matsayin Sabon Shugaban APC

WAKILIN MU by WAKILIN MU
July 24, 2025
in Labarai
A A
0

 

Jam’iyyar APC ta zaɓi Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Zaɓen ya gudana ne a ranar Alhamis yayin zaman Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar, inda aka zaɓe shi ba tare da hamayya ba don maye gurbin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya sauka daga muƙamin bisa wasu dalilai na lafiya.

Yilwatda, wanda aka haifa a ranar 8 ga Agusta, 1968 a garin Dungung, Ƙaramar Hukumar Kanke ta Jihar Filato, fitaccen masani ne a fannin aikin injiniyan na’ura mai ƙwaƙwalwa da lantarki.

Ya yi karatun sa na farko a Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Makurdi, sannan ya samu digirin sa na biyu daga ATBU Bauchi, da kuma digirin digirgir daga Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka.

Ya kwashe sama da shekaru 26 yana koyarwa da gudanar da manyan ayyuka a jami’o’i, kuma ya taka rawa a matsayin daraktan ICT na farko a Jami’ar Makurdi.

Baya ga aikin ilimi, Farfesan ya taka rawa a ɓangaren ƙirƙire-ƙirƙire da sauyi ta fannin fasaha a ciki da wajen gwamnati. A matsayin sa na ƙwararre a harkar sadarwa da fasahar zamani, ya yi aiki da manyan ƙungiyoyin duniya irin su EU, UNICEF, Bankin Duniya da Techville USA.

A shekarar 2017, ya zama Kwamishinan Zaɓe na INEC, inda ya kawo muhimman sauye-sauye a tsarin zaɓe da suka haɗa da tsarin kaɗa ƙuri’a ga ’yan gudun hijira da masu buƙata ta musamman.

Yanzu da ya zama shugaban APC na ƙasa, Yilwatda ya shigo da ƙwarewa ta musamman, hangen nesa, da sadaukarwa da zai amfani jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya.

A matsayin sa na shugaban kamfen ɗin Tinubu/Shettima a Jihar Filato, kuma Ministan Jinƙai, yana da zurfin alaƙa da ɓangarori da dama na gwamnati da ƙungiyoyin cigaba, wanda ake da ran hakan zai taimaka wajen jagorantar jam’iyyar cikin haɗin kai da nasara.

Previous Post

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

Next Post

WAFU 2025: Gwamnatin Tarayya Ta Yabi Super Falcons a Matsayin Zakarun Afrika

Related Posts

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu
Labarai

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu

October 1, 2026
Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Next Post

WAFU 2025: Gwamnatin Tarayya Ta Yabi Super Falcons a Matsayin Zakarun Afrika

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!