Gwamnatin Tarayya ta nuna cikakken goyon bayan ta ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles gabanin wasan kusa da na ƙarshe na gasar AFCON da za su fafata da takwarar su ta ƙasar Marokko, inda ta tabbatar wa da ’yan wasan cewa ɗaukacin al’ummar ƙasar nan suna tare da su.
Da ƙarfe 9 na daren yau Laraba ne dai za a fafata tsakanin Nijeriya da Marokko a birnin Rabat.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ’yan wasan ƙasar da su ci gaba da mayar da hankali, sannan su yi amfani da nasarorin da suka samu zuwa yanzu a matsayin makamin tunkarar wasan.
Ministan ya ce: “Ya ku Super Eagles, yayin da kuke shirin fafatawa da Momarokko a wasan kusa da na ƙarshe, ina son ku sani cewa ɗaukacin Nijeriya tana tare da ku. Bajintar da kuka nuna zuwa yanzu abin alfahari ne. Wasa bayan wasa, kuna nuna ƙwazo, juriya, da yaƙini, kuna tunatar da mu dalilin da ya sa Super Eagles take ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da aka fi girmamawa a Afrika.”
Ya tunatar da ’yan wasan irin ɗaukakar da Nijeriya take da ita a fagen ƙwallon ƙafa na nahiyar, inda ya bayyana cewa nasarorin da aka samu a baya sun samo asali ne daga haɗin kai, ƙwarin gwiwa, da jajircewa.
Idris ya ce: “Kun taɓa kaiwa wannan mataki a baya, kuma kun san abubuwan da ake buƙata don samun nasara a mataki irin wannan. Tun daga kofunan AFCON da kuka taɓa ɗagawa zuwa ga manyan ƙungiyoyin da kuka yi nasara a kan su, ko yaushe kuna ɗaga tutar Nijeriya cikin alfahari.
“Waɗannan nasarorin ba haka nan aka same su ba; sakamakon aiki tare ne, da ƙwarin gwiwa, da kuma ruhin fafatawa. Kun nuna wannan ruhi a wannan gasa ma.”
Ministan ya ƙarfafa wa ƙungiyar gwiwa da su shiga fili da ƙwarin gwiwar zakaru, yana mai jaddada cewa miliyoyin ‘yan Nijeriya suna samun ƙwarin gwiwa daga ƙwazon da suke nunawa.
“Yayin da kuka shiga cikin fili, ku sani cewa ba ku kaɗai ba ne. Kuna ɗauke da fatan miliyoyin ‘yan Nijeriya. Sun amince da ku, kuma suna samun ƙwarin gwiwa daga bajintar da kuke nunawa.
“Ku buga wasa da ƙwarin gwiwar zakaru, da haɗin kan ’yan’uwan juna, da kuma kishin cin nasara. Ku tuna tarihin ɗaukakar ku da kuma ƙimar da kuke da ita,” inji shi.
Yayin da yake kira ga nuna tsantsar sadaukarwa, Idris ya buƙaci ’yan wasan da su kasance masu mayar da hankali da jajircewa har zuwa ƙarshen wasan.
“Ku mai da hankali, ku yarda da juna, sannan ku bayar da dukkan ƙarfin ku tun daga farkon wasa har zuwa ƙarshe. Ku ci kowace ƙwallo, ku fafata don samun kowace dama. Kada ku taɓa kokwanto kan abin da za ku iya cimma muddin kuna tare. Kun cancanci kaiwa wannan mataki, kuma kuna da dukkan ƙwarewar da zai kai ku ma fiye da haka,” inji shi.
Daga ƙarshe, ya ƙalubalanci Super Eagles da su sake ba ƙasar alfahari.
“A daren yau, ku fita ku rubuta wani sabon babi na alfahari a tarihin ƙwallon ƙafar Nijeriya. Ku buga da zuciya ɗaya. Ku buga cikin alfahari. Ku buga domin Nijeriya. Allah ya yi muku albarka, Super Eagles. Allah ya albarkaci Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya,” inji shi.







