Shugaba Recep Tayyip Erdogan na ƙasar Turkiyya, ya bayyana aniyar ƙasar sa na saka jarin da ya kai dala biliyan 5 a fannin kasuwanci a Nijeriya.
Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Ankara, babban birnin ƙasar, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, lokacin da ya kai ziyarar aiki ta Shugaban a Turkiyya.
Ya ce an soma tattaunawa kan cimma wannan buri tare da amincewa da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, domin faɗaɗa damar kasuwanci da ƙarfafa zuba jarin ‘yan kasuwar Turkiyya a Nijeriya.
Ya yaba da jajircewa da ƙudirin Tinubu wajen jawo zuba jari, yana mai cewa halartar ministoci da manyan jami’ai daga Nijeriya wata bayyananniyar shaida ce ta wannan aniya.
A cewar sa: “Mun yi cikakken nazari kan dangantakar mu da Shugaban Nijeriya da tawagar sa, musamman a fannonin kasuwanci, zuba jari, makamashi, ilimi da masana’antar tsaro. Mun tattauna matakan da za a ɗauka domin cimma burin dala biliyan 5, tare da tallafa wa zuba jari a Nijeriya. Mun yi imanin cewa kafa Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci zai taka muhimmiyar rawa.”
Shugaba ya yaba da sauye-sauyen da Tinubu yake jagoranta a fannin makamashi, wanda ya taimaka wajen sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya.
Ya yi fatan cewa haɗin gwiwar Kamfanin Man Fetur na Turkiyya (TPAO) da abokan aikin sa a Nijeriya zai haifar da sakamako mai kyau.
Dangane da barazanar ta’addanci a Nijeriya da yankin Sahel, Erdogan ya tabbatar da goyon bayan Turkiyya, yana mai cewa ƙasar sa tana da ƙwarewa a yaƙi da ta’addanci.
Ya ce: “Ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Sahel na barazana ga zaman lafiyar Afrika baki ɗaya. Muna tare da al’ummar Nijeriya a wannan yaƙi, kuma a shirye muke mu ƙara haɗin gwiwa a fannonin horas da sojoji da musayar bayanan sirri.”
A nasa jawabin, Tinubu ya nuna godiya ga Turkiyya kan buɗaɗɗiyar zuciya da shirin ta na haɗin gwiwa domin ƙarfafa ‘yanci, zaman lafiya da walwala a duniya.
Ya jaddada muhimmancin gina tattalin arziki da ya haɗa kowa da kowa, musamman masu rauni.

Ya ce: “Abu mafi muhimmanci shi ne kasuwanci ba tare da shinge ba, da ba wa masu son aiki da koyo dama. Ta yaya za mu gina tattalin arziki da ya haɗo kowa da kowa? Ta yaya za mu shigar da masu rauni cikin tattalin arziki? Ta yaya za mu tabbatar da zaman lafiya a duniya?”
Shugaban ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta ci gaba da taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afrika, duk da ƙalubalen tsaro da ke yankin.
A ƙarshen taron, ƙasashen biyu sun yi yarjejeniyoyi guda tara, ciki har da:
– Yarjejeniya kan manufofin ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje
– Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tsaro
– Sanarwar Kafa Kwamitin Tattalin Arziki da Kasuwanci
– Yarjejeniya kan ingantaccen tsarin Halal
– Haɗin gwiwa a fannonin ilimi, kafofin watsa labarai da sadarwa
– Haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatun Harkokin Waje da na Harkokin Mata da Jinƙai na ƙasashen biyu.






