Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya karɓi baƙuncin tawagar Cibiyar Zuba Jari ta Ƙasa da Ƙasa ta Birtaniya, wato British International Investment (BII), a ranar Laraba.
Tawagar na ƙarƙashin jagorancin shugaban su, Diana Layfield, kuma sun samu rakiyar Jakaden Birtaniya a Nijeriya, Mista Richard Montgomery.
Haɗuwar ta CBN da BII dai wani hoɓɓasa ne domin ƙara ƙarfi da ingancin sauye-sauye da tsare-tsaren kuɗaɗe, domin ƙara jawo ɗimbin masu zuba jari daga waje, kuma a daɗe ana cin moriyar juna.
Cardoso ya ƙara jaddada jajircewar da CBN ke yi wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya bisa nagartacciya hanya mai ɗorewa. Sai kuma tafiya ɗoɗar bisa ƙaƙƙarfan tsarin bankuna mai jure ƙalubale.
Ga hotunan ziyarar.








