• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya jajanta wa zakaran damben boksin Anthony Joshua da mahaifiyar sa ta wayar tarho kan mummunan haɗarin da ya yi

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
December 29, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya jajanta wa zakaran damben boksin Anthony Joshua da mahaifiyar sa ta wayar tarho kan mummunan haɗarin da ya yi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Anthony Joshua a Fadar Shugaban Ƙasa a watannin baya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Anthony Joshua a Fadar Shugaban Ƙasa a watannin baya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana ta wayar tarho a yau da Anthony Joshua, tsohon zakaran damben boksin na ajin heavyweight ɗan Nijeriya da Birtaniya, wanda mummunan haɗari ya ritsa da shi a Jihar Ogun, inda Joshua ya jikkata kuma abokan tafiyar sa biyu suka rasu.

Wata sanarwa ga manema labarai da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar da yammacin yau ta ruwaito Tinubu yana cewa: “Na yi magana da AJ ta wayar tarho domin in isar masa da ta’aziyya ta da kai na bisa rasuwar abokan sa biyu. Na yi masa fatan alheri tare da yi masa addu’a. Ya tabbatar mini cewa yana samun kulawa mafi kyau a asibiti.

“Har ila yau, na yi magana da mahaifiyar AJ, na yi mata addu’a. Ta nuna matuƙar godiya bisa kiran da na yi mata.

“Bugu da ƙari, na yi magana da Gwamna Dapo Abiodun, wanda ke asibiti tare da su. Gwamnan ya tabbatar mini cewa zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa AJ ya samu kulawa mafi inganci.”

Tun da farko, a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Shugaba Tinubu—wanda ke ƙasashen waje a halin yanzu—ya bayyana matuƙar juyayin sa ga ɗan damben kan haɗarin da ya faru da shi a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Ya ce: “Ina jajanta maka kai da iyalan ka yayin da kuke ɗauke da nauyin baƙin cikin wannan mummunan lamari. A matsayin ka na ɗan wasa, a ko da yaushe ka nuna jarumta, ladabi, da ƙaunar ƙasa mara yankewa. Waɗannan halaye ne da suka sa ka zama abin alfaharin ƙasa.

“A irin waɗannan lokuta, ya kamata mu ƙarfafa juna a matsayin ’yan’uwa maza da mata masu rabon makoma ɗaya.

“Ina roƙon Allah ya ba ka ƙarfi, hikima, da rahama a wannan lokaci mai raɗaɗi. Allah ya ba ka sauƙin murmurewa cikin gaggawa, ya kuma jiƙan waɗanda suka rasu.”

Tags: Anthony JoshuahaɗarijajeShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Yadda bankin CBN ya hana ‘yan Nijeriya fuskantar ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna yayin hutun ƙarshen shekara

Next Post

Wani abu ya fashe a asibitin Bagudo da ke Kebbi

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Wani abu ya fashe a asibitin Bagudo da ke Kebbi

Wani abu ya fashe a asibitin Bagudo da ke Kebbi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!