Rundunar ’yan sanda a Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an samu fashewar wani abu da sanyin safiyar yau Talata a Babban Asibitin Bagudo da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo ta jihar.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi, ya ce: “Muna so mu tabbatar wa da dukkan mazauna yankin cewa ana da cikakken iko kan halin tsaro bayan wata ƙara mai ƙarfi ta fashewar wani abu da aka ji a Babban Asibitin Bagudo da sanyin safiyar Talata, 30 ga Disamba.
“Haɗin gwiwar jami’an tsaro na ’yan sanda, sojoji da ’yan banga sun gaggauta killace tare da tabbatar da tsaron yankin da abin ya shafa. Ƙwararrun jami’an EOD-CBRN suna wurin suna gudanar da cikakken bincike.
“Muna farin cikin tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ran sa ko ya jikkata. Duk da cewa wani gini a gidajen ma’aikata ya lalace, mazaunan sun riga sun fice lafiya.
“Kwamishinan ’yan sanda na jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya.”
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa CP ya tabbatar wa da al’umma cewa ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ce: “Muna roƙon jama’a da su kwantar da hankalin su tare da guje wa kusantar wurin da abin ya faru domin bai wa jami’an tsaro da masu bincike damar ci gaba da aikin su. Za mu ci gaba da bayar da ƙarin bayani idan buƙatar hakan ta taso.”






