• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyara a Legas

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 6, 2025
in Labarai
A A
0
Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba – Idris
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja yau bayan shafe kwanaki 10 na ziyarar aiki a Jihar Legas.

Shugaban ya je Legas a ranar Juma’a, 26 ga Satumba, bayan halartar bikin nadin sabon Olubadan na Ibadan, Mai Martaba Oba Rashidi Adewolu Ladoja.

A yayin da yake Lagos, Shugaban Ƙasa ya gana da manyan ’yan kasuwa da masu zuba jari, ciki har da shugaban kamfanin Global Infrastructure Partners, Bayo Ogunlesi, da tsohon shugaban UBA da Etisalat, Akeem Belo-Osagie, wanda yanzu ke shugabantar Metis Capital Partners.

Shugaba Tinubu ya kuma karɓi baƙuncin Sakatare-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Duniya (IMO), Mista Arsenio Dominguez, tare da Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola, da shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar.

A yayin tattaunawar, Shugaban Ƙasa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na inganta harkokin ruwa a matsayin hanyar dena dogaro da man fetur.

A daren bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, Shugaban Ƙasa ya ziyarci Jihar Imo, inda ya ƙaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar.

Haka kuma ya halarci taron kaddamar da littafin da Gwamnan ya rubuta kan tarihin shekaru 10 na mulkin jam’iyyar APC a Nijeriya.

A ranar bikin ’yancin kai, Shugaban Ƙasa ya gabatar da jawabin ƙasa kai tsaye daga fadar gwamnati ta Dodan Barracks.

Daga bisani kuma, ya ƙaddamar da sabunta Gidan wasa na ƙasa (National Theatre), wanda yanzu aka sake masa suna zuwa Cibiyar Al’adu da Fasaha ta Wole Soyinka (Wole Soyinka Centre for Culture and the Creative Arts), inda ya yi kira ga ’yan ƙasa da su riƙa yin fata mai kyau game da Nijeriya.

A ranar Asabar, 4 ga Oktoba, Shugaban Ƙasa ya ziyarci garin Jos, Jihar Filato, domin halartar jana’izar mahaifiyar Farfesa Nantawe Yilwatda, Shugaban APC na ƙasa.

A wajen jana’izar, Shugaba Tinubu ya yaba da rayuwa da jajircewar marigayiya Mama Lydia Yilwatda, tare da tabbatar wa al’ummomin Kiristoci na Arewa cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tabbatar da adalci da daidaito tsakanin mabiya mabambantan addinai a faɗin ƙasar nam.

Previous Post

Gwamnatin Tinubu na ci gaba da tallafa wa manoman Arewa da kayan aikin gona 

Next Post

Tinubu ya bada umarnin a rage kuɗin kujerar aikin Hajji na 2026

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Tinubu ya bada umarnin a rage kuɗin kujerar aikin Hajji na 2026

Tinubu ya bada umarnin a rage kuɗin kujerar aikin Hajji na 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!