Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da ta rage kuɗin kujerar aikin Hajji na shekara ta 2026 domin darajar Naira ta inganta a kasuwar musayar kuɗi.
A sakamakon wannan umarni, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bai wa hukumar wa’adin kwana biyu don fitar da sabon tsarin kuɗin kujerar aikin Hajji da zai dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar nan.
Shettima ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa yayin taron da ya jagoranta tare da shugabannin NAHCON da wasu jami’an gwamnati, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an jihohi da gwamnoni wajen tabbatar da sabon tsarin da ya dace.
Ya kuma buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta biyan kuɗaɗen da suka wajaba da aika su ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara da tsari.
Da yake bayani ga manema labarai bayan taron, Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadeija, ya ce manufar taron ita ce kammala shirye-shiryen aikin Hajji na 2026, musamman batun kuɗin kujera.
Ya ce, “Tun da darajar Naira ta samu ƙaruwa a kasuwa saboda gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ke yi, dole ne hakan ya bayyana a cikin kuɗin aikin Hajji. Idan masu aikin Hajji sun biya Naira miliyan 8.5 zuwa Naira miliyan 8.6 a bara saboda raguwar darajar Naira, yanzu da ta inganta, dole ne su amfana da sauƙin kuɗin.”
Shi ma Sakataren NAHCON, Dakta Mustapha Mohammad, ya ce umarnin shugaban ƙasa zai ƙara yawan masu niyyar zuwa Hajji a bana.
A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi, kuma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumar Alhazai ta Jihohi da Birnin Tarayya, Alhaji Faruk Aliyu Yaro, ya bayyana farin cikin sa da wannan mataki.
Ya ce, “Muna murna sosai da wannan mataki da shugaban ƙasa da mataimakin sa suka ɗauka. Mun yi imanin hakan zai rage farashin kujerar Hajji kuma ya sauƙaƙa wa Musulmi.”







