• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ya yi murabus bayan watanni ana artabu da shi

ALI KANO by ALI KANO
February 11, 2026
in Labarai
A A
0
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ya yi murabus bayan watanni ana artabu da shi
Farfesa Abdullahi Saleh Usman

Farfesa Abdullahi Saleh Usman

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi murabus daga muƙamin sa.

Mai taimaka masa kan fasaha, Ahmed Mu’azu, ya tabbatar wa jaridar The Guardian murabus ɗin a safiyar yau Talata, inda ya ce aje aikin ya fara aiki ne tun daga jiya Litinin. Ba a bayar da wani dalili a hukumance ba kan matakin.

Usman, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a shekarar 2024, ya jagoranci aikin Hajji na farko a ƙarƙashin sa a shekarar 2025, wanda ya zama karon farko da ya kula da harkokin aikin Hajjin Nijeriya a matakin ƙasa.

An naɗa shi ne domin maye gurbin Jalal Arabi, wanda aka cire daga muƙamin yayin da ake binciken sa kan zargin karkatar da kuɗaɗen da aka fitar domin Hajjin 2024.

Sai dai, ɗan gajeren zaman sa a muƙamin ya fuskanci rikice-rikice na cikin gida da kuma zarge-zargen da suka shafi tafiyar da kuɗi da gudanarwa a lokacin aikin Hajjin 2025. Waɗannan matsaloli sun haddasa tashin hankali a cikin hukumar tare da jawo hankalin jama’a.

Rikicin ya kai ƙololuwa ne a watan jiya, lokacin da wasu kwamishinonin NAHCON suka miƙa takarda ga Shugaba Tinubu, inda suka kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da shugabancin Farfesan.

A cikin takardar da suka rubuta ranar 19 ga Janairu, kwamishinonin sun zarge shi da rashin bin ƙa’idojin tafiyar da kuɗi, rashin gaskiya, karya dokokin saye da sayarwa na gwamnati, da kuma aikata wasu abubuwa da suka saɓa da dokokin kuɗin hukumar.

Sun kuma yi zargin cewa an bayar da wasu kwangiloli ba tare da samun takardar “No Objection Certificate” daga Hukumar Kula da Saye da Sayarwa ta Gwamnati (BPP) ba, sannan an kashe wasu kuɗaɗe ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa ba.

Takardar ta kuma ambaci rahotannin da ke cewa ana binciken shugaban ne daga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).

A cewar kwamishinonin, wannan hali ya haifar da rashin jituwa a cikin NAHCON tare da barazana ga shirye-shiryen Hajjin 2026.

Rikicin ya ja hankalin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya kira taro da manyan masu ruwa da tsaki domin sasanta ɓangarorin da ke rikici tare da dawo da zaman lafiya a cikin hukumar.

Rahotannin baya sun kuma nuna zargin kurakurai na gudanarwa a Hajjin 2025, ciki har da cewa dubban gadon da aka biya a Mina, Saudiyya, sun kasance ba a yi amfani da su ba, inda ake zargin ba a mayar da kuɗaɗen da ya kamata cikin wa’adin da aka tanada ba.

Shugaban dai ya ƙaryata zarge-zargen, yana mai cewa sun samo asali ne daga rikicin cikin gida.

Murabus ɗin Usman ya ƙara jefa jagorancin NAHCON cikin rashin tabbas a wani lokaci mai muhimmanci, yayin da shirye-shiryen Hajjin 2026 ke ƙara ɗaukar zafi.

Tags: FarfesaAbdullahiSalehUsmanHajjiHajji2026murabusNAHCONzargi
Previous Post

Kamfanin BUA Foods ya naɗa Khalifa Rabi’u muƙamin zartarwa yayin da yake ƙara ƙaimi kan bunƙasa kasuwanci

Next Post

Gwamnati ta naɗa Ambasada Isma’il Yusuf Abba a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Gwamnati ta naɗa Ambasada Isma’il Yusuf Abba a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa

Gwamnati ta naɗa Ambasada Isma'il Yusuf Abba a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!