• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati ta naɗa Ambasada Isma’il Yusuf Abba a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa

ALI KANO by ALI KANO
February 11, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnati ta naɗa Ambasada Isma’il Yusuf Abba a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa
Ambasada Isma'il Yusuf Abba, sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa

Ambasada Isma'il Yusuf Abba, sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa

Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar naɗin Ambasada Isma’il Yusuf Abba a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), bisa jiran amincewar Majalisar Dattawa.

Wannan na zuwa ne bayan murabus ɗin Farfesa Abdullahi Saleh Usman a ranar Litinin.

An ba da sanarwar wannan sabon naɗi a yau.

Mataimakiyar Darakta, Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta bayyana cewa Yusuf, wanda tsohon jami’in diflomasiyya ne a Ma’aikatar Harkokin Waje, shi ne Jakadan Nijeriya na baya-bayan nan a ƙasar Turkiyya.

An haife shi a ranar 7 ga Yuli, 1962 a Mubi, Jihar Adamawa. Ya kammala karatu a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato a shekarar 1985 inda ya samu digiri a fannin Kimiyyar Siyasa.

Ya yi hidimar ƙasa (NYSC) a Cibiyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adanai da Noma ta Ijebu a 1986, sannan nan take aka ɗauke shi aiki a Ma’aikatar Harkokin Waje a Disamban 1986.

Yusuf ya halarci manyan kwasa-kwasan ƙwarewa, kuma ya kai matsayi Darakta a shekarar 2013.

Daga bisani, a 2021 aka naɗa shi Jakada Mai Cikakken Iko kuma Na Musamman a Jamhuriyar Turkiyya.

Usara ta ce: “Ambasada Yusuf ya taka muhimmiyar rawa wajen hanzarta dangantakar dabaru da Turkiyya, musamman a fannonin tsaro, kare ƙasa, kasuwanci da zuba jari, da haɗin gwiwar masana’antu.”

Ta ƙara da cewa ƙwarewar sa ta ginu ne kan gogewa mai tsawo ta tsawon shekaru 35 na aikin gwamnati da aka rubuta a tarihi.

A tsawon zamanin aikin sa, ya yi aiki a ofisoshi daban-daban, ciki har da ofisoshin jakadancin Nijeriya a Ajantina, Italiya da Chana.

A hedikwata kuwa, ya riƙe muƙamai daban-daban a sassa kamar nazari, ayyuka, horaswa, gudanarwa, da kuma harkokin alhazai, inda ya jagoranci sakatariyar Kwamitocin Shugaban Ƙasa kan Hajji (PCH) daga 2002 zuwa 2007.

Kwamitin PCH yana da alhakin ƙirƙiro, tsara da aiwatar da ingantattun manufofi domin tabbatar da tafiyar aikin Hajji cikin sauƙi ga Musulman Nijeriya zuwa Saudiyya a kowace shekara.

Ayyukan kwamitin ne suka shimfiɗa tubali da tsarin kafa NAHCON da kuma fara aikin ta cikin nasara a 2006, inda Yusuf ya kuma yi aiki a matsayin sakataren jadawalin ayyuka.

Tun da fari a 2005, ya kasance sakataren wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya da ta je nazarin yadda ake gudanar da harkokin Hajji a Malesheya da Indonesiya.

An yi hakan ne bisa ga gagarumar ƙwarewa da ingancin da ƙasashen biyu suka nuna a harkokin Hajji tsawon shekaru.

Sakamakon binciken tawagar ya ba da gudunmawa sosai ga farkon ayyukan NAHCON, musamman wajen kafa Tsarin Ajiya na Hajji (Hajj Savings Scheme).

Yusuf ya kuma kasance Sakataren tawagogin Gwamnatin Tarayya guda biyu (Amirul Hajj) a shekarun 2012 da 2013.

Daga 2011 zuwa 2013, bayan an tura shi Fadar Shugaban Ƙasa, ya yi aiki a matsayin Mataimaki na Musamman kan Harkokin Shugaban Ƙasa a ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa (Chief of Staff). Ayyukan sa sun haɗa da taƙaita da nazarin takardun bayanai (memos), da kuma taimaka wa Shugaban Ma’aikata wajen tsara shirye-shiryen Shugaban Ƙasa.

Ambasada Yusuf yana jin harsunan Hausa, Yarbanci, Igala, Turanci da Sifaniyanci.

Usara ta ce shugabannin NAHCON sun yi maraba da wannan sabon naɗi, tare da bayyana shirin su na bai wa sabon shugaban cikakken goyon baya, sannan ta buƙaci ma’aikata da masu ruwa da tsaki da su ba da haɗin kai da goyon baya.

“Wannan yana da matuƙar muhimmanci musamman a daidai lokacin da shirye-shiryen aikin Hajjin bana suka kai wani mataki na gaba,” inji ta.

Tags: alhazaiFatimaSandaUsaraHajjiIsma'ilYusufAbbaNAHCONnaɗi
Previous Post

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ya yi murabus bayan watanni ana artabu da shi

Next Post

CBN ya umurci bankuna da su riƙa sayar wa ‘yan canji dala 150,000 a kowane mako

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
CBN ya tashi haiƙan: Malejin farashin kayayyaki ya ƙara yin ƙasa zuwa kashi 16.05, yayin da asusun kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 46.7

CBN ya umurci bankuna da su riƙa sayar wa 'yan canji dala 150,000 a kowane mako

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!