• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Kamfanin BUA Foods ya naɗa Khalifa Rabi’u muƙamin zartarwa yayin da yake ƙara ƙaimi kan bunƙasa kasuwanci

ALI KANO by ALI KANO
February 10, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Kamfanin BUA Foods ya naɗa Khalifa Rabi’u muƙamin zartarwa yayin da yake ƙara ƙaimi kan bunƙasa kasuwanci
Alhaji Isyaku Abdulsamad Rabi'u (Khalifa)

Alhaji Isyaku Abdulsamad Rabi'u (Khalifa)

Kamfanin BUA Foods Plc ya naɗa Alhaji Isyaku Abdulsamad Rabi’u (wanda aka fi sani da sunan Khalifa) a matsayin babban jami’i mai kula da saye-da-sayarwa na duniya da ayyukan dabaru.

Kamfanin ya yi haka ne domin ƙarfafa sahun shugabannin sa yayin da yake sake fasalin samar da kayayyaki tare da neman bunƙasa cikin ingantaccen tsari mai rahusa.

Kamfanin ya ce naɗin Khalifa ya fara aiki ne daga ranar 29 ga Janairu, 2026.

Matashin ɗan kasuwar zai jagoranci dukkan harkokin saye-da-sayarwa na duniya daga farko har ƙarshe na kamfanin, tare da jagorantar shirye-shiryen inganta ayyuka domin ƙara ƙwarewa, rage farashi da kuma ƙarfafa juriya a wajen samar da kayayyaki a dukkan fannoni na kamfanin.

Wannan mataki ya zo ne yayin da BUA Foods ke sauyawa daga matakin daidaitawa zuwa abin da ya bayyana a matsayin bunƙasa mai tsari da faɗaɗa aiki a manyan sassan kayan abincin sa, ciki har da fulawa, taliyar makaroni, shinkafa da abincin dabbobi.

Khalifa dai ya fito ne daga uwar rukunin kamfanonin, wato BUA Group, inda ya riƙe muƙamin darakta mai kula da ayyuka na musamman, kuma ya jagoranci shirye-shiryen sauyi da dama a ɓangarorin abinci, siminti da abincin dabbobi.

Kamfanin ya ce aikin sa ya haɗa da ƙarfafa alaƙa da masu samar da kayayyaki, inganta tsarin saye-da-sayarwa da kuma haɓaka ingancin ayyuka.

A cewar kamfanin, Khalifa ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara sayen albarkatun ƙasa, musamman alkama, tare da jagorantar kafa wata masana’antar sarrafa abincin dabbobi mai ƙarfin samar da tan 40 a cikin awa guda kacal.

Bugu da ƙari, ya kuma shiga cikin sake dawo da kayayyakin shinkafar BUA a kasuwar masu amfani ta Nijeriya, tare da kula da ƙaddamar da dandamali na dijital mallakar kamfanin a dukkan ayyukan BUA Foods.

Manajan Daraktan BUA Foods, Ayodele Abioye, ya faɗa a cikin wata sanarwa a yau cewa: “Yayin da BUA Foods ke shiga sabon matakin sauyi, wanda ke nuna sauyawa daga daidaita kasuwanci zuwa bunƙasa mai tsari da faɗaɗa aiki, muna farin cikin maraba da Khalifa cikin tawagar shugabannin mu.

“Ƙwarewar sa a fannin saye-da-sayarwa ta duniya da ayyukan dabaru za ta taimaka sosai wajen ƙarfafa tsarin samar da kayayyakin mu da kuma haɓaka ingancin ayyuka.”

A wani nazari da ta yi kan labarin, jaridar BusinessDay ta yi la’akari da cewa gudanar da tsarin samar da kayayyaki ya zama muhimmin abu ga masana’antun abinci a Nijeriya, waɗanda suka fuskanci tashin-tashinar kasuwar canjin kuɗaɗen waje, hauhawar farashin kayan masarufi da matsalolin sufuri a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ta ce kamfanoni suna ƙoƙarin tabbatar da wadatattun albarkatun ƙasa da kuma inganta tsarin saye-da-sayarwa domin kare ribar su da daidaita samarwa.

A nasa ɓangaren, Khalifa ya ce yana shirin haɓaka tsarin saye-da-sayarwa mai sassauci da ɗorewa domin tallafa wa burin kamfanin na dogon lokaci.

Ya ce: “Ina matuƙar farin ciki da karɓar wannan muƙami a wannan muhimmin lokaci na tafiyar bunƙasar BUA Foods.

“Ina fatan jagorantar dabarun saye-da-sayarwa da ayyuka da za su tallafa wa manufofin kamfanin na dogon lokaci.”

Khalifa Rabi’u yana da digirin farko a fannin hulɗar ƙasashe daga Jami’ar Regent’s da ke London, da digiri na biyu a fannin gudanarwa daga Makarantar Kasuwanci ta McDonough da ke Jami’ar Georgetown a Amurka.

Kamfanin BUA Foods, mallakin attajiri Abdul Samad Rabi’u, ya faɗaɗa ayyukan sa cikin sauri a ‘yan shekarun nan, inda ya zuba jari a cikin samar da kayayyaki a cikin gida da kuma faɗaɗa ƙarfin masana’antu domin rage dogaro da shigo da kaya daga waje da kuma inganta sarrafa farashi.

Wannan naɗin na Khalifa ya nuna sabon ƙudirin mayar da hankali kan aiwatarwa da bin ƙa’idojin gudanarwa yayin da kamfanin yake shirin shiga sabon matakin bunƙasa.

Tags: AbdulSamadRabiuBUAFoodsBUAGroupkasuwanciKhalifaRabiunaɗi
Previous Post

Tinubu ya naɗa Magaji Da’u Aliyu a matsayin shugaban cibiyar binciken nukiliya ta ƙasa, ya kuma sabunta shugabancin NEMSA

Next Post

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ya yi murabus bayan watanni ana artabu da shi

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ya yi murabus bayan watanni ana artabu da shi

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ya yi murabus bayan watanni ana artabu da shi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!