• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

 Nijeriya ta samu amincewar UNESCO ta gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta ta farko

* Mazaunin Cibiyar zai kasance a jami’ar NOUN, Abuja

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 5, 2025
in Ilimi
A A
0
 Nijeriya ta samu amincewar UNESCO ta gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta ta farko
Hagu zuwa dama: Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Ƙasa (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo; Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Sanata Injiniya Kenneth Eze; Jakadiyar Nijeriya a UNESCO, Dakta Hajo Sani; Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ƙa’idoji da Halaye; Ɗan Majalisa Olusola Fatoba; Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Malam Abdulhamid Salihu Dembos; da Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace, a wajen Babban Taron na UNESCO na 43 (na Hukumar Sadarwa da Bayanai) a birnin Samarkand, ƙasar Uzbekistan, a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025. Hoto daga: Khalid Ahmed

Ƙungiyar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta Ƙasa da Ƙasa a Abuja, Nijeriya, a matsayin Cibiyar UNESCO ta Rukuni na Biyu, wadda ita ce irin ta ta farko a duniya.

A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mai Taimaka wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa UNESCO ta bayar da wannan muhimmiyar amincewa ne a Babban Taro na 43 na Hukumar Sadarwa da Bayanai da aka gudanar a birnin Samarkand na ƙasar Uzbekistan.

Cibiyar za ta kasance ne a hedikwatar Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) da ke Abuja.

Ibrahim ya ce: “Da wannan amincewar, yanzu Nijeriya ta zama jagora a duniya wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya a kafafen sada zumunta, tare da samun damar jagorantar bincike, tattauna manufofi da gina ƙwarewa a wannan muhimmin fanni na zamani.”

A jawabin da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya gabatar a taron na UNESCO, ya bayyana wannan cigaba a matsayin “wata alamar yarda da girmamawa ga ƙasar mu.”

Ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta ɗauki wannan nauyi da muhimmanci, inda ya bayyana cewa cibiyar za ta zama matattarar bincike da ilimi ta duniya domin taimaka wa jama’a da al’umma su iya tafiya cikin duniyar dijital cikin hankali da tabbaci.

Ministan ya ce: “Gwamnatin Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta himmatu wajen gina al’umma wadda ke ganin ’yancin faɗar albarkacin baki a matsayin ginshiƙin cigaban ƙasa.

“Babban ginshiƙin wannan manufar shi ne bai wa kowa damar shiga fagen fasahar zamani, tare da ilimin kafofin watsa labarai a matsayin ginshiƙin cigaba.”

Ya bayyana cewa wannan nasara ta biyo bayan doguwar tafiya da ta faro tun a watan Oktoba 2022, lokacin da Nijeriya ta karɓi baƙuncin taron duniya na 10 kan Ilimin Kafofin Watsa Labarai a Abuja, inda ta yi alƙawarin kafa irin wannan cibiya ta UNESCO a ƙasar.

Ya ce: “Ina amfani da wannan dama in taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murna bisa wannan nasara, wadda ke nuna jajircewar sa wajen ganin an cimma manufofin Shirin Sabunta Fata. Wannan nasara ce ba kawai ga Nijeriya ba, har ma ga nahiyar Afrika baki ɗaya.”

Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da UNESCO domin cika buƙatun cibiyar ta fuskar gina kayayyakin more rayuwa da kuma samar da ƙwararrun masana daga fannoni daban-daban domin tabbatar da nasarar wannan aikin.

Ya kuma bayyana cewa bikin ƙaddamar da cibiyar zai gudana ne a Fabrairu 2026 a Abuja, tare da halartar jami’an UNESCO, wakilan ƙasashe mambobi da abokan hulɗa daga sassa daban-daban na duniya.

Cikin tawagar da ta halarci Babban Taron na 43 na UNESCO domin shaida amincewar da aka bai wa IMILI Nijeriya a matsayin Cibiyar UNESCO ta Rukuni na Biyu, akwai Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Sanata Injiniya Kenneth Eze; Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Yaɗa Labarai, Ƙa’idoji da Halaye, Hon. Olusola Fatoba; Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama, wanda ya wakilci Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai; Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Malam Abdulhamid Salihu Dembos; Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Tarayya (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo; Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; da Jakadiyar Nijeriya a UNESCO, Dakta Hajo Sani, tare da wasu jami’an gwamnatin Nijeriya.

Tags: IMILIUNESCO
Previous Post

Yadda Tinubu ya magance tsadar abinci ba tare da samun cikas ga Shirin Farfaɗo da Noma a Nijeriya ba

Next Post

Gwamnati ta yi raddi kan matakin Amurka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini

Related Posts

Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba
Ilimi

Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba

October 12, 2026
Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja
Ilimi

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

August 29, 2026
Ilimi

Niger-SUBEB ta tabbatar da ƙarin girma ga malaman da suka cancanta

August 22, 2026
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris
Ilimi

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

August 20, 2026
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki
Ilimi

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

August 4, 2026
Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya
Ilimi

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

July 16, 2026
Next Post
Gwamnati ta yi raddi kan matakin Amurka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini

Gwamnati ta yi raddi kan matakin Amurka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!