• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati ta yi raddi kan matakin Amurka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini

Wakilin Mu by Wakilin Mu
November 5, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnati ta yi raddi kan matakin Amurka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa a Abuja a yau Laraba

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa a Abuja a yau Laraba

Nijeriya ta bayyana rashin jin daɗin ta kan matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na sanya ƙasar nan cikin jerin ƙasashen da ake ganin suna take ’yancin yin addini.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa a Abuja a yau Laraba.

Idris ya ce gwamnatin Nijeriya ta san irin damuwar da wannan mataki na Amurka ya haifar, musamman ma bayan furucin Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar kawo wa Nijeriya farmaki bisa hujjar bada kariya ga Kiristoci.

Ministan ya jaddada cewa matsalolin tsaro da Nijeriya take fuskanta ba su taɓa bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba, inda ya ce: “Ta’addanci ba ya da addini, ba ya kallon ƙabila ko matsayi. Yaƙi ne da dukkan mutanen da ke son zaman lafiya a Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai na zahiri don kawo ƙarshen matsalar tsaro, kuma tun bayan hawan sa mulki a watan Mayu 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna tsantsar niyyar sa ta tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan.

A cewar ministan, sojojin Nijeriya sun kashe sama da ’yan ta’adda 13,500, tare da kama fiye da 17,000 da ake ci gaba da binciken su da shari’a a kan su, haka kuma an ceto mutum 9,800 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara.

Idris ya bayyana cewa sauyin da aka yi wa manyan hafsoshin tsaro da kuma sake tsara tsarin tsaro a ƙasar suna daga cikin matakan da Tinubu ya ɗauka don kawo ƙwarin gwiwa da inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

“Manufar ita ce a tabbatar da cewa kowace kusurwa ta Nijeriya ta samu tsaro, kuma kowanne ɗan ƙasa ya rayu cikin kwanciyar hankali,” inji shi.

Idris ya kuma bayyana cewa an samu raguwar hare-haren ta’addanci sosai, musamman a Arewa-maso-gabas da Arewa-maso-yamma, tare da raunin kashi 80 cikin 100 na hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a Kudu-maso-gabas.

Gwamnati ta ce an kama wasu manyan shugabannin ƙungiyoyin ta’addanci kamar Mahmud Muhammad Usman da Abubakar Abba na ƙungiyar Ansaru, da kuma Khalid Al-Barnawi, wanda ake zargi da kitsa harin ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Abuja a 2011.

Ya ƙara da cewa mutum 125 daga cikin waɗanda ake zargi da ta’addanci sun riga sun samu hukunci, yayin da wasu ɗaruruwan suke ci gaba da fuskantar shari’a a kotuna daban-daban.

Ministan ya ce duk da matakin Amurka, Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da Amurka da sauran ƙasashe domin kawar da ta’addanci.

Ya ce: “Muna fatan Amurka za ta fahimci cewa Nijeriya ƙasa ce mai girma, mai ɗimbin al’adu da addinai, wadda ke samun cigaba a fannin tsaro da tattalin arziki.”

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya samar da jiragen yaki na Super Tucano da ake amfani da su wajen yaƙi da ’yan ta’adda, kuma nan gaba kaɗan ana sa ran ƙarin jirage masu sarrafa makamai za su iso ƙasar.

A ƙarshe, Idris ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.

“Nijeriya tana hannun aminci da shugabanci mai cike da ƙwarin gwiwa. Shugaba Tinubu na jagorantar tsaro, cigaban tattalin arziki da zaman lafiya mai ɗorewa, inji shi.”

Tags: barazanaDonald TrumpMohammed Idris
Previous Post

 Nijeriya ta samu amincewar UNESCO ta gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta ta farko

Next Post

Jimamin Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Jimamin Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa

Jimamin Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, Tsohon Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!