• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Nijeriya da Tarayyar Turai sun ƙaddamar da shirin ilimi da ƙarfafa wa matasa gwiwa a Arewa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 15, 2025
in Ilimi
A A
0
Nijeriya da Tarayyar Turai sun ƙaddamar da shirin ilimi da ƙarfafa wa matasa gwiwa a Arewa
Mahalartan taron

Mahalartan taron

Gwamnatin Nijeriya da Tarayyar Turai (EU) sun ƙaddamar da wani sabon shiri na ilimi da ƙarfafa wa matasa gwiwa mai darajar Yuro miliyan 40 domin inganta harkar ilimi a yankin Arewa-maso-yamma na ƙasar nan.

An gudanar da taron ne a Abuja, inda Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Abel Olumuyiwa Enitan, wanda Dakta Ejeh Usman ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin ginshiƙin manufar ‘Renewed Hope Agenda’ ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ‘Education Sector Renewal Initiative’ da ke nufin tabbatar da dama ga kowa wajen samun ingantaccen ilimi.

Shugabar sashen ilimi na matakin farko, Dakta (Mrs) Folake Davies Olatunji, ta ce shirin zai mayar da hankali ne wajen koyar da ilimi tun daga tushe, horar da malamai, inganta ilimin zamani ta hanyar fasaha da kuma bayar da damar ilimi ga kowa.

Ana tattaunawa a taron

A nata jawabin, wakiliyar EU, Miss Kate Kanebi, ta tabbatar da jajircewar Tarayyar Turai, inda ta bayyana cewa kuɗin da ya kai naira biliyan 69.9 za su taimaka wajen samar da tsare-tsaren karatu cikin aminci, koyar da sana’o’in dogaro da kai musamman ga mata da marasa galihu.

Cibiyoyi irin su UBEC, TRCN, UNESCO, UNICEF, Plan International, Save the Children da kuma Bankin Duniya sun halarci taron.

A ƙarshe, taron ya kammala da alƙawari haɗin gwiwa wajen tabbatar da ilimi mai inganci da ya shafi kowa a faɗin ƙasar nan.

Wani sashe a taron
Previous Post

Cewar Minista: Gwamnati ta saki da naira biliyan 32.9 don inganta kiwon lafiya

Next Post

Tinubu ya kawo sauye-sauye masu haifar da gagarumin cigaba ga Nijeriya — Idris

Related Posts

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
Gwamnatin Tarayya ta fara horas da matasa 260,000 a fannoni daban-daban na sana’o’in dogaro da kai
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa kiran kan su ‘Dakta’

May 6, 2026
Ku daina kira na Bahaushe, cewar Bishop Kukah ga ’yan Nijeriya
Ilimi

Ku daina kira na Bahaushe, cewar Bishop Kukah ga ’yan Nijeriya

April 26, 2026
NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795
Ilimi

NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795

April 19, 2026
Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi
Ilimi

Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi

March 15, 2026
Gwamnatin Tarayya ta fara horas da matasa 260,000 a fannoni daban-daban na sana’o’in dogaro da kai
Ilimi

Gwamnatin Tinubu ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikatan koyar da sana’o’i a Kwalejojin Fasaha

February 18, 2026
Next Post
Tinubu ya kawo sauye-sauye masu haifar da gagarumin cigaba ga Nijeriya — Idris

Tinubu ya kawo sauye-sauye masu haifar da gagarumin cigaba ga Nijeriya — Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!