Gwamnatin Tarayya ta amince da wata manufa da ta haramta wa waɗanda aka ba digirin girmamawa amfani da taken “Dakta”.
Wannan mataki, wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da shi, ya kafa sabon tsarin doka da zai jagoranci bayarwa da amfani da digirin girmamawa a manyan makarantun gaba da sakandare, tare da hukunci ga masu karya dokar.
Da yake magana a Abuja ranar Laraba, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon damuwa kan yadda ake ƙara yin mummunan amfani da kuma siyasantar da digirin girmamawa.
Alausa ya ce manufar wannan gyara ita ce kare mutuncin ilimi, dawo da amincewar jama’a ga lambobin yabo na jami’o’i, da kuma daƙile yadda ake cin zarafi da mayar da digirin girmamawa tamkar harkar kasuwanci.
Ya ce gwamnati ta lura da wani “abin damuwa” inda wasu jami’o’i suke ba da digirin girmamawa ba tare da tsari ba, har ma ga jami’an gwamnati masu aiki, sannan wasu daga cikin waɗanda aka karramawa ɗin suna amfani da taken “Dakta” a harkokin hukuma da na jama’a.
“Ana sa ran waɗanda aka ba wannan digiri su ɗauke shi a matsayin lambar yabo ko karramawa, ba a matsayin cikakkiyar takardar shaidar ilimi ba,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa bayyana digirin girmamawa tamkar takardar shaidar ilimi zai kasance zambar ilimi, wanda zai jawo sakamakon doka da kuma ɓata suna.
Alausa ya ce jami’o’in da ke da ingantaccen tsarin bayar da digirin PhD ne kawai za a ba damar bayar da digirin girmamawa, yana mai cewa yadda sababbin cibiyoyin ilimi da ba su da shirye-shiryen digirin digirgir ke bayar da irin wannan lambar yabo “ba daidai ba ne.”
Ya kuma ce sabuwar manufar ta ƙarfafa Sanarwar Keffi (Keffi Declaration) da kwamitin shugabannin jami’o’in Nijeriya ya ƙirƙiro domin daƙile cin zarafi wajen bayar da digirin girmamawa.
Game da aiwatarwa, ministan ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ta hannun Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), za ta fitar da ƙa’idoji, sa ido kan bukukuwan yaye ɗalibai, tare da wallafa jerin sunayen halal na waɗanda aka ba digirin girmamawa a kowace shekara.
“Za mu haɗa kai da kafafen yaɗa labarai domin hana danganta taken ilimi ba bisa ƙa’ida ba ga mutanen da aka ba digirin girmamawa,” inji shi.
Da yake mayar da martani kan damuwar da ake da ita game da ‘yancin cin gashin kan jami’o’i, Alausa ya ce dole ne cibiyoyin ilimi su yi aiki cikin iyakar doka.
“Cin gashin kai ba yana nufin ikon karya doka a wannan ƙasa ba,” inji ministan.
Ita ma da take magana, Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta ce Sanarwar Keffi tun asali shugabannin jami’o’i ne suka ƙirƙiro ta a matsayin jagora, amma ba ta da ƙarfin doka.
Ta ce amincewar Gwamnatin Tarayya yanzu ta ba sanarwar cikakken ƙarfin hukuma, wanda zai ba da damar aiwatar da ita yadda ya kamata.
Majalisar ta kuma amince da kafa asusun bunƙasa bincike da ƙirƙire-ƙirƙire na ƙasa, domin ƙarfafa haɗin kai a ɓangaren bincike a Nijeriya da kuma daidaita zuba jari da manufofin cigaban ƙasa.






