• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya kawo sauye-sauye masu haifar da gagarumin cigaba ga Nijeriya — Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
October 15, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya kawo sauye-sauye masu haifar da gagarumin cigaba ga Nijeriya — Idris
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da gwamnonin APC a wajen tashar samar da wuta ta gaggawa ta Maiduguri mai ƙarfin 50MW, wadda gwamnatin Buhari ta ƙaddamar, kuma gwamnatin Tinubu ta ƙara inganta ta

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da gwamnonin APC a wajen tashar samar da wuta ta gaggawa ta Maiduguri mai ƙarfin 50MW, wadda gwamnatin Buhari ta ƙaddamar, kuma gwamnatin Tinubu ta ƙara inganta ta

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tsarin sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa yana haifar da sakamako mai kyau, wanda ke bai wa gwamnatocin jihohi damar gudanar da ayyuka masu amfani kai-tsaye ga jama’a.

Idris ya bayyana hakan ne a Maiduguri, Jihar Borno, a ranar Laraba, yayin da ya jagoranci kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohin da jam’iyyar APC ke mulki a wani zagayen duba muhimman ayyukan Gwamnatin Tarayya da na jihohi, wanda wani sashe ne na taron musamman wata hurhuɗu da suke yi a jihohi.

Ministan ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun ƙara yawan kuɗaɗen da ake tura wa jihohi, wanda ya ba su damar aiwatar da manyan ayyuka masu tasiri ga rayuwar talakawa.

Ya ce: “Ina tabbatar muku da cewa ajandar sauye-sauyen Shugaban Ƙasa na aiki yadda ya kamata. Yana ƙara wa jihohi kuɗaɗe domin su yi amfani da su wajen yi wa jama’a aiki.”

Tawagar ta ziyarci sabuwar cibiyar bada lantarki ta hasken rana mai ƙarfin 12MW a Jami’ar Maiduguri, wadda Hukumar Samar Da Wutar Lantarki a Karkara (REA) tare da goyon bayan Bankin Duniya ta gina.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammed Mele, ya bayyana cewa wannan cibiya tana wadatar da jami’ar da asibitin koyarwa da wutar lantarki, tare da rage musu kashe kuɗin wuta da kusan naira miliyan 170 a duk wata.

Haka kuma, tawagar ta duba tashar samar da wuta ta gaggawa ta Maiduguri mai ƙarfin 50MW, wadda gwamnatin Buhari ta ƙaddamar, kuma gwamnatin Tinubu ta ƙara inganta ta, tana samar da wuta ko da yaushe ga gidaje da masana’antu a cikin birnin da kewaye.

Yayin da yake jaddada nasarorin da Gwamnatin Jihar Borno ta samu, Idris ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa gina manyan makarantun zamani guda 104 da ya yi a dukkan mazaɓun sanata uku na jihar cikin shekara guda, yayin da aka kusa kammala guda 35.

Yayin da suka kai ziyara a ɗaya daga cikin makarantun da aka sanya wa sunan Shugaban Ƙasa Tinubu, Idris ya ce wannan shiri yana nuna yadda gyare-gyaren da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa suke ba jihohi damar zuba jari a fannin ilimi da makomar yaran Nijeriya.

Sauran ayyukan da aka ziyarta sun haɗa da gadar sama ta Borno Express Terminus, wadda za ta zama gada ta huɗu da gwamnatin jihar ta gina, inda aikin ya fara tun a farkon wannan shekara.

Idris ya ce wannan nasara alama ce ta haɗin gwiwa mai kyau tsakanin Gwamnatin Tarayya da na jihohi.

“Wannan shi ne abin da haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da na jihohi zai iya haifarwa,” inji shi.

Tawagar ta kuma ziyarci tashar cajin motocin lantarki ta Herwa EV Station — ɗaya daga cikin tashoshi bakwai da gwamnatin Jihar Borno ta kafa tare da goyon bayan Hukumar Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC).

Idris ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufar Gwamnatin Tarayya ta ƙaura zuwa tsaftataccen makamashi da sababbin hanyoyin samar da wuta.

A ƙarshe, aikin gina sabon sashen ƙasa da ƙasa na Babban Filin Jirgin Sama na Muhammadu Buhari, Maiduguri, yana ci gaba da tafiya.

Shugaba Tinubu ya amince da haɓaka filin zuwa na ƙasa da ƙasa a watan Maris 2025, wanda hakan ya sanya shi zama shi kaɗai irin sa a yankin Arewa-maso-gabas.

Tags: APCBornogwamnoniMohammed Idrissauye-sauyeShugaba Bola Ahmed Tinubuwutar lantarki
Previous Post

Nijeriya da Tarayyar Turai sun ƙaddamar da shirin ilimi da ƙarfafa wa matasa gwiwa a Arewa

Next Post

Cewar Minista: Borno ta fi kowace jiha juriya a Nijeriya

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Cewar Minista: Borno ta fi kowace jiha juriya a Nijeriya

Cewar Minista: Borno ta fi kowace jiha juriya a Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!