• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Nijeriya da ɗimbin ƙasashe sun amince da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa

* Ƙasashe takwas kacal ne suka kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da ƙudirin majalisar

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
December 16, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Nijeriya da ɗimbin ƙasashe sun amince da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa
Yankunan Falasɗinu ne masu jar kala

Yankunan Falasɗinu ne masu jar kala

Nijeriya a ranar Litinin ta bi sahun yawancin ƙasashen duniya wajen kaɗa ƙuri’a domin goyon bayan wani ƙudiri da ke sake jaddada haƙƙin Falasɗinawa na kafa ƙasar su ta kan su.

Babbar Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri’a tare da amincewa da ƙudirin da ke tabbatar da haƙƙin kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kan ta.

Jimillar ƙasashe membobi 164, ciki har da dukkan ƙasashen Afrika 54 da ke cikin Majalisar Ɗinkin Duniya, sun kaɗa ƙuri’ar goyon bayan ƙudirin.

Gaba ɗaya, ƙasashe takwas ne kawai suka kaɗa ƙuri’ar adawa da ƙudirin. Waɗannan su ne: Isra’ila, Amurka, Micronesia, Argentina, Paraguay, Papua New Guinea, Palau, da Nauru.

Ƙudirin ya sake jaddada matsayar Majalisar Ɗinkin Duniya da aka daɗe a kan ta, wadda ke tabbatar da haƙƙin al’ummar Falasɗinu na kafa ƙasar su da kuma bin ci gaban tattalin arziki, zamantakewa da al’adu.

Haka kuma, ƙudirin ya yi kira ga dukkan ƙasashe, hukumomi na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran sassan tsarin MDD da su ci gaba da ba da goyon baya da taimako ga al’ummar Falasɗinu domin a hanzarta tabbatar da wannan haƙƙi.

Ya kuma jaddada buƙatar mutunta haɗin kai na yanki, ci gaba da jere-jeren ƙasa da cikakken ikon yankunan Falasɗinu da aka mamaye, ciki har da Gabashin Ƙudus.

Wannan ƙudiri ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta goyi bayan wani ƙudiri da ke buƙatar Isra’ila ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba kan isar da agajin jinƙai zuwa Zirin Gaza.

Majalisar ta kuma buƙaci Isra’ila da ta dakatar da kai hare-hare kan wuraren Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da bin dokokin ƙasa da ƙasa, bisa la’akari da wajibcin ta a matsayin ta na ƙasar mamaya.

Sai dai Jakaden Isra’ila a Majalisar Ɗinkin Duniya, Danny Danon, ya zargi majalisar da amincewa da wani ƙudiri da ke tilasta Isra’ila yin aiki da ta’addanci.

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya daɗe yana ƙin amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu.

Nijeriya tana daga cikin ƙasashen da suka sha yin kira da a samar da tsarin ƙasashe biyu domin kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila da Hamas, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban Falasɗinawa.

A Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a watan Satumba, Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce dole ne a bai wa Falasɗinawa ’yanci da mutunci iri ɗaya da wanda ake bai wa sauran ’yan ƙasashen duniya.

Yayin da yake jawabi a gaban majalisar, Shettima ya ce al’ummar Falasɗinu ba su cancanci ci gaba da fuskantar rikice-rikice na dogon lokaci da kuma mummunan bala’in jinƙai da suka sha ba.

“Su ma mutane ne, daidai daraja, kuma sun cancanci irin ’yanci da mutunci da muke ɗauka a matsayin abu na kowa,” inji shi.

A yayin taron, wasu ƙasashen Turai da dama, ciki har da Birtaniya, Kanada da Ostiraliya, sun amince da Falasɗinu a hukumance a matsayin ƙasa mai cin gashin kan ta.

Cikin fushi, Mista Netanyahu ya bayyana matakin nasu a matsayin “kyautar banza ga ta’addanci.”

Ya sha alwashin cewa “ba za a kafa Ƙasar Falasɗinu a yammacin Kogin Jodan ba.”

Ya kuma ce Isra’ila za ta ci gaba da yaƙi a Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran dandalin ƙasa da ƙasa domin tunkarar abin da ya kira da “ƙaryar farfaganda.”

Tags: FalasɗinuIsra'ilaMajalisar Ɗinkin Duniyaƙuri'a
Previous Post

Ɗangote ya maka shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed a ICPC bisa zargin cin hanci da rashawa

Next Post

Bankwana da 2025: Yadda tsare-tsaren CBN ya saukar da malejin hauhawar farashi zuwa kashi 14.45 a ƙarshen shekara

Related Posts

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta
Ƙasashen Duniya

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

April 3, 2026
Next Post
Bankwana da 2025: Yadda tsare-tsaren CBN ya saukar da malejin hauhawar farashi zuwa kashi 14.45 a ƙarshen shekara

Bankwana da 2025: Yadda tsare-tsaren CBN ya saukar da malejin hauhawar farashi zuwa kashi 14.45 a ƙarshen shekara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!