• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ɗangote ya maka shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed a ICPC bisa zargin cin hanci da rashawa

ALI KANO by ALI KANO
December 16, 2025
in Labarai
A A
0
Turnuƙu kan fetur: Ɗangote ya fallasa cikakkun bayanai kan makarantun da ’ya’yan shugaban NMDPRA suka halarta a Switzerland
Daga hagu: Aliko Ɗangote da Farouk Ahmed

Daga hagu: Aliko Ɗangote da Farouk Ahmed

Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya miƙa ƙorafi kan Darakta-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Mai na Cikin Teku ta Nijeriya (NMDPRA), Injiniya Ahmed Farouk, ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC), inda ya zarge shi da cin hanci da rashawa da almundahana ta kuɗi.

A cikin ƙorafin da ya miƙa a ranar 16 ga Disamba, Ɗangote ya nemi a kama, a binciki kuma a gurfanar da Ahmed a kotu bisa zargin rayuwa sama da ƙarfin albashin sa a matsayin sa na ma’aikacin gwamnati.

A ƙorafin da ofishin Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN), ya karɓa, Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote ɗin ya zargi shugaban na NMDPRA da kashe kuɗi ba tare da hujjar halastacciyar hanyar samun kuɗin ba, da ya kai sama da dala miliyan 7, domin biyan kuɗin karatun ’ya’yan sa huɗu a makarantu daban-daban a ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida.

A cikin takardar ƙorafin, Ɗangote ya ambaci sunayen ’ya’yan huɗu da makarantun da suke karatu a Switzerland, tare da adadin kuɗin da aka biya wa kowannen su, domin tabbatar da zarge-zargen da kuma sauƙaƙa tantancewa daga hukumar ta yaƙi da cin hanci.

Ya yi zargin cewa Farouk Ahmed yana amfani da hukumar NMDPRA wajen wawurewa da karkatar da kuɗaɗen jama’a domin amfanin kan sa da cimma muradun kan sa na sirri, abin da ya jawo hayaniya da zanga-zanga daga ƙungiyoyi daban-daban a kwanakin baya, wanda ya cutar da al’ummar Nijeriya.

Ɗangote ya ƙara da cewa Farouk Ahmed, a tsawon rayuwar sa ta balaga, ya yi aiki ne a ɓangaren gwamnati a Nijeriya, kuma jimillar kuɗin shigar sa a tsawon shekarun ba ta kai kusa da dala miliyan 7 ba, wanda ake zargin an karkatar da su daga baitulmalin jama’a domin biyan kuɗin karatun ’ya’yan sa matasa a ƙasar waje.

“Babu shakka cewa waɗannan bayanai da suka shafi cin zarafin muƙami, karya Dokar Ladabi ga Ma’aikatan Gwamnati, tara dukiya ta haram, da almundahana, manyan ayyukan cin hanci da rashawa ne, waɗanda hukumar ku (ICPC) take da ikon doka a ƙarƙashin sashe na 19 na Dokar ICPC, don bincike da gurfanarwa,” inji Ɗangote.

Ya ƙara da cewa: “Bayan samun nasarar gurfanar da irin wannan mutum, a ƙarƙashin sashe na 19 na Dokar ICPC, yana fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba.

“Muna faɗa da ƙarfin gwiwa cewa ICPC tana da matsayi mai ƙarfi tare da sauran hukumomi ’yan’uwan ta wajen gurfanar da laifukan kuɗi da sauran laifukan cin hanci da rashawa, kuma da zarar an tabbatar da hujjar farko (prima facie), kotuna ba sa jinkirin hukunta mai laifi.

“Saboda haka, muna kiran hukumar a ƙarƙashin jagorancin ku da ta binciki ƙorafin cin zarafin muƙami da cin hanci da rashawa da ake yi wa Injiniya Farouk Ahmed, tare da gurfanar da shi idan aka same shi da laifi.

“Ba mu da wata shakka cewa kasancewar wannan lamari yana gaban jama’a, hukumar ba za ta rufe ido ba, sai ta ɗauki mataki mai tsauri domin tabbatar da adalci da kare kyakkyawan mutuncin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Ɗangote dai ya sha alwashin kasancewa a shirye domin gabatar da hujjoji don tabbatar da zarge-zargen sa na tara dukiya ta hanyar haram da cin zarafin muƙami da yake yi wa Injiniya Farouk Ahmed.

Tags: Aliko Dangotecin hancinFarouk AhmedICPCrashawazargi
Previous Post

Turnuƙu kan fetur: Ɗangote ya fallasa cikakkun bayanai kan makarantun da ’ya’yan shugaban NMDPRA suka halarta a Switzerland

Next Post

Nijeriya da ɗimbin ƙasashe sun amince da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Nijeriya da ɗimbin ƙasashe sun amince da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa

Nijeriya da ɗimbin ƙasashe sun amince da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!