• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ku Ƙara Haƙuri, Cewar Tinubu Yayin Ƙaddamar Da Kashin Farko Na Titin Bakin Teku Na Legas Zuwa Kalaba

ALI KANO by ALI KANO
May 31, 2025
in Labarai
A A
0
Ku Ƙara Haƙuri, Cewar Tinubu Yayin Ƙaddamar Da Kashin Farko Na Titin Bakin Teku Na Legas Zuwa Kalaba
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ƙaddamar da titin bakin teku na Legas zuwa Kalaba... a Legas a yau.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ƙaddamar da titin bakin teku na Legas zuwa Kalaba... a Legas a yau.

* Ya Ƙaddamar Da Wasu Hanyoyin

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki domin jin daɗi yana nan tafe.

Ya faɗi haka ne a yau Asabar lokacin da yake ƙaddamar da babban titin bakin teku da ya tashi daga Legas zuwa Kalaba, tare da shan alwashin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shirye domin amfanuwar ‘yan Nijeriya.

Ya ce: “Ina roƙon dukkan ‘yan Nijeriya kan cewa kyakkyawar fata tana tare da mi. Tattalin arzikin mu yana farfaɗowa.”

Ya yi nuni da yadda ake samun daidaito a musanyar kuɗi sannan kuma farashin kayan abinci yana raguwa.

Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da wasu manyan hanyoyin a faɗin ƙasar nan.

A bikin ƙaddamarwar wanda aka yi a Legas a yau, Tinubu ya umarci Ministan Ayyuka, David Umahi, da sauran ministoci da ke kula da ayyukan da ake aiwatarwa a sassan ƙasar nan da su riƙa bin dokar nan da ta gindaya sharaɗin yin amfani da kayan aikin da ake da su cikin ƙasar, da horas da ‘yan Nijeriya da kuma sauyin fasaha.

Kashin farko na titin bakin teku na Legas zuwa Kalaba da Tinubu ya ƙaddamar a yau

Gwamnonin jihohin Legas, Delta, Ogun, Edo, Bayelsa, Borno, Ekiti, Kogi, Ondo, Kuros River, da Imo sun halarci taron.

Babban marubuci, Farfesa Wole Soyinka, da Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ‘ya’yan Chagoury, da ‘yan kwangilar hanyar su ma sun halarta.

Manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu, da Ciyaman ɗin UBA Group, Tony Elumelu, sun halarta.

Previous Post

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa

Next Post

Tinubu Ya Tura Wakilai Zuwa Neja Kan Ambaliyar Mokwa Da Ta Halaka Sama Da Mutum 150

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
Next Post
Tinubu Ya Tura Wakilai Zuwa Neja Kan Ambaliyar Mokwa Da Ta Halaka Sama Da Mutum 150

Tinubu Ya Tura Wakilai Zuwa Neja Kan Ambaliyar Mokwa Da Ta Halaka Sama Da Mutum 150

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!