• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Isra’ila tana aiki kan wani shiri na tallafa wa Kiristocin Nijeriya, in ji Netanyahu

ALI KANO by ALI KANO
January 2, 2026
in Labarai
A A
0
Isra’ila tana aiki kan wani shiri na tallafa wa Kiristocin Nijeriya, in ji Netanyahu
Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Isra’ila

Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Isra’ila

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ƙasar sa tana aiki kan wata ajanda domin tallafa wa al’ummomin Kirista “da ke fama da matsin lamba a Nijeriya.”

Netanyahu ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin wani taro da shugabannin al’ummar Kiristoci masu wa’azi a jihar Florida ta ƙasar Amurka, inda ya bayyana Isra’ila a matsayin ƙasar da ita kaɗai ce ke da ikon kare Kiristoci a duniya.

Ya ce: “Na ga yaƙin da ake yi da mu da kuma yaƙin da ake yi da al’adar Yahudawa da Kiristoci, wanda a zahiri ana gwabzawa a duk faɗin duniya. Kuma ana gwabza shi ne musamman ta hannun ƙarfi biyu — Musuluncin Shi’a mai tsattsauran ra’ayi da kuma Musuluncin Sunni mai tsattsauran ra’ayi.

“Wannan na nufin gungun da Iran ke jagoranta, wanda aka raunana sosai, gaskiya ne, amma har yanzu yana nan, da kuma gungun Sunni da ƙungiyar Muslim Brotherhood ke jagoranta, wadda ta kutsa cikin komai.

“Suna zuwa Turai, suna zuwa Amurka, suna zuwa Afrika, Nijeriya. Kuma muna sane da gaskiyar cewa ana tsananta wa Kiristoci — a faɗin Gabas ta Tsakiya, a Siriya, a Lebanon, a Nijeriya, a Turkiyya da ma bayan haka.

“Muna kuma sane da gaskiyar, kamar yadda ku ma kuka sani, cewa ƙasa ɗaya ce kawai ke kare al’ummar Kirista — tana ba su damar bunƙasa, tana kare su, tana tabbatar da cewa suna ci gaba — kuma wannan ƙasar ita ce Isra’ila. Babu wata ƙasa daban. Babu ko ɗaya.

“Muna shiga wani ƙoƙari na kafa, a zahiri, ƙungiyar ƙasashe ko ƙasashen da ke tallafa wa al’ummomin Kirista a duk duniya — al’ummomin da ke cikin hali na matsi waɗanda suka cancanci taimakon mu.

“Kamar yadda kuke taimaka mana, mu ma muna son mu taimaka muku; kuma muna da ikon yin haka. A Afrika, ta hanyar bayanan sirri, a Gabas ta Tsakiya kuma da hanyoyi da dama da ba zan lissafa su ɗaya bayan ɗaya ba.

“Wannan ita ce ajandar mu; muhimmin ɓangare ne na ajandar mu.”

Jawaban na Netanyahu sun zo ne kwana guda bayan ganawar sa da Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya bada sanarwar kai hare-haren sama a Nijeriya a ranar Kirsimeti domin cika barazanar sa ta tsoma bakin soja don dakatar da abin da ya kira tsananta wa Kiristoci a ƙasar.

A ranar da aka kai hare-haren, Netanyahu ya ce dole ne a kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Nijeriya.

Isra’ila ita ce kaɗai ƙasar da ta fito fili ta goyi bayan Amurka kan iƙirarin da ta yi na “matsa wa Kiristoci” a Nijeriya.

Dukkan ƙasashen biyu an san su da kasancewa abokan ƙawance na ƙut da ƙut da juna.

Tags: Benjamin NetanyahuIsra'ilaKiristociNijeriya
Previous Post

Za mu zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin murƙushe barazanar tsaro a 2026 – Tinubu

Next Post

Kotu ta sake tsare Malami, ɗan sa da matar sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Kotu ta sake tsare Malami, ɗan sa da matar sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Kotu ta sake tsare Malami, ɗan sa da matar sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!