• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotu ta sake tsare Malami, ɗan sa da matar sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

ALI KANO by ALI KANO
January 2, 2026
in Labarai
A A
0
Kotu ta sake tsare Malami, ɗan sa da matar sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje
Alhaji Abubakar Malami, SAN

Alhaji Abubakar Malami, SAN

Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Maitama, Abuja, a wannan Juma’ar ya sake bayar da umurnin tsare tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da ɗan sa, Abubakar Abdul’aziz Malami, da matar sa, Hajiya Asabe Bashir, a Gidan Gyaran Hali na Kuje, Abuja, har zuwa ranar 7 ga Janairu, 2026, domin yanke hukunci kan buƙatun su na beli.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da waɗanda ake tuhuma bisa zargin aikata laifukan wanke kuɗi da adadin su ya kai N8,713,923,759.49 (naira biliyan takwas da miliyan ɗari bakwai da goma sha uku da dubu ɗari tara da ashirin da uku da naira ɗari bakwai da hamsin da tara da kobo arba’in da tara).

An gurfanar da su a kan tuhume-tuhume 16 da suka shafi haɗin baki, sayo, ɓoye, rufe gaskiya da wanke kuɗaɗen da aka samu ta haramtattun ayyuka, saɓanin tanade-tanaden Dokar Hana da Kare Wanke Kuɗi ta shekarar 2022.

A zaman kotun da aka ci gaba da yi a yau Juma’a, lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Ekele Iheanacho, SAN, ya sanar da kotu cewa an tanadi zaman ne domin sauraron buƙatar beli da waɗanda ake tuhuma suka shigar.

Da yake mayar da martani, lauyan waɗanda ake tuhuma, J.B. Daudu, SAN, ya shaida wa kotu cewa gwamnati ta yi musu hidimar takardar amsa (counter affidavit) ne a kotu a ranar, don haka suna buƙatar lokaci su karanta su kuma su mayar da martani yadda ya dace.

Bayan duba takardar, Daudu ya shigar da wata takardar amsa mai sakin layi kusan 28 zuwa 30, yana ƙalubalantar dalilan da ya sa bai kamata a ci gaba da tsare waɗanda ake tuhuma ba.

A nasa ɓangaren, Iheanacho ya shaida wa kotu cewa su ma an yi musu hidimar wata takardar amsa ne yanzu, don haka suka nemi lokaci su nazarci takardun.

Ya ce: “An yi mana hidimar takardar amsa kuma mun nemi lokaci domin duba takardun, ranka ya daɗe.

“Yanzu kuma an yi mana hidimar wata ƙarin takarda, kowannen su na ɗauke da sakin layi kusan 28 zuwa 30, tare da amsa kan hujjojin shari’a. Ban kai ga dubawa ba, kuma ina buƙatar lokaci.”

Da yake mayar da martani, lauyan waɗanda ake tuhuma ya ce: “Ran ka ya daɗe, an dage shari’ar zuwa yau, kuma akwai ranar aiki a tsakani. Ban san dalilin da ya sa ba su yi mana hidima ba tun da wuri. Ba shi da amfani ga gwamnati ta ci gaba da tsawaita tsare mutanen. Ba su da haƙkin sake bayar da amsa. Idan yana buƙatar mintuna 15 zuwa 20, kotu za ta iya ba shi.”

Ya ƙara da cewa ya dace a yi amfani da ladabi na ƙwararru, yana jaddada shirin sa na ci gaba da shari’ar.

A nasa martanin, Iheanacho ya bayyana cewa: “Ran ka ya daɗe, duk da cewa ba burin mu ba ne waɗanda ake tuhuma su daɗe a tsare ba tare da dalili ba, kuma a matsayi na na babban lauya a ƙungiyar lauyoyi, ina da girmamawa matuƙa ga aboki na lauya. Amma yanzu ne aka yi min hidimar takardu uku, kowanne yana ɗauke da sakin layi kusan 28 zuwa 30. Ya fi kyau a yi gaggawa cikin taka-tsantsan.”

Bayan muhawara tsakanin lauyoyin, kuma ba tare da wata adawa ba, kotu ta soke wata buƙata tare da amincewa da wata bisa roƙon lauyan kare.

Da yake gabatar da buƙatun beli, Daudu ya roƙi kotu da ta ba da beli ga waɗanda ake tuhuma na ɗaya, na biyu da na uku, yana roƙon a ba wa wanda ake tuhuma na farko beli bisa dogaro da kan sa, yayin da na biyu da na uku a ba su beli bisa sharuɗɗa masu sauƙi.

Ya ce: “Ran ka ya daɗe, game da wanda ake tuhuma na farko, tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, bukaytar tana tare da takardar shaida mai sakin layi 36 da ɗan sa, Nuzain Malami, ya rantse a kai a ranar 29 ga Disamba, 2025, tare da shaidu guda shida da aka sanya wa alamar Exhibits A1, B, C da E, da kuma jawabin rubuce.”

Ya ƙara da cewa buƙatar beli ta wanda ake tuhuma na biyu tana tare da takardar shaida mai sakin layi 28 da ‘yar ta, Farida Abdullahi Usman, ta rantse a kai, tare da shaidu A da B, da kuma jawabi a rubuce mai kwanan wata 29 ga Disamba, 2025.

Buƙatar na uku kuma, inji shi, tana tare da takardar shaida mai sakin layi 39 da ɗan’uwan sa, Nuzain Malami, ya rantse a kai.

Daudu ya jaddada cewa laifukan suna da damar beli, kuma doka ta ɗauki waɗanda ake tuhuma a matsayin marasa laifi har sai an tabbatar da laifin su.

Ya yi watsi da zargin tsoma baki ga shaidu a matsayin zato kawai, yana nuna cewa tun farko EFCC ta ba su beli na gudanarwa.

“Ba daidai ba ne wata hukuma ta ba da beli a baya sannan yanzu ta yi jayayya akasin haka,” inji shi, yana roƙon kotu ta yi amfani da ikon ta wajen amfanin waɗanda ake tuhuma.

Da yake adawa da buƙatun, Iheanacho ya shaida wa kotu cewa EFCC ta shigar da takardun amsa guda uku daban-daban kan waɗanda ake tuhuma a ranar 2 ga Janairu, 2026, waɗanda Adebayo Daniel, jami’in hukumar, ya rantse a kan su, tare da jawabai a rubuce.

“Ran ka ya daɗe, bayanan da ke cikin takardun amsa, musamman game da lalata shaidu da tsoma baki da shaidu da wanda ake tuhuma na farko da na biyu suka yi, ba a ƙaryata su ba,” inji shi, yana dogaro da hujjojin shari’a cewa abubuwan da ba a ƙaryata ba ana ɗaukar su a matsayin an amince da su.

Ya kafa hujjar cewa tsoma baki da shaidu na lalata tushen shari’a adalci, tare da roƙon kotun da ta yi la’akari da tanade-tanaden Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka (ACJA) wajen ƙin bayar da beli.

Game da batun beli na gudanarwa da aka bayar a baya, gwamnati ta ce beli kafin shari’a yayin bincike ya bambanta da beli yayin shari’a bayan an shigar da tuhume-tuhume.

“Ɗaukar mutum a matsayin mara laifi ba ya ba shi tikitin beli kai-tsaye,” inji gwamnati, tana roƙon kotu ta ƙi buƙatun.

A taƙaice, Mai Shari’a Nwite ya lura da yawan ayyukan da ke gaban kotu a lokacin hutun shari’a, amma ya tabbatar da cewa za a yi adalci cikin gaggawa.

“Ina da shari’o’i masu yawa da suka shafi manyan mutane a wannan lokacin hutu, amma za a yi adalci cikin mafi ƙanƙantar lokaci,” inji shi.

Daga nan sai ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 7 ga Janairu, 2026, domin yanke hukunci kan buƙatun beli.

Tags: Abubakar MalamiEFCCkotuKuje
Previous Post

Isra’ila tana aiki kan wani shiri na tallafa wa Kiristocin Nijeriya, in ji Netanyahu

Next Post

Kisan gilla a Borgu: ’Yan bindiga sun kashe mutum 42, sun sace da dama a Jihar Neja

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Kisan gilla a Borgu: ’Yan bindiga sun kashe mutum 42, sun sace da dama a Jihar Neja

Kisan gilla a Borgu: ’Yan bindiga sun kashe mutum 42, sun sace da dama a Jihar Neja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!